Tun daga farkon karni na Sha bakwai ( K17) zuwa farkon karni na Sha tara ( K19) Kasar Katsina ta kasashence babbar cibiyar kasuwanci ta Kasar Hausa ( Transharan Trade Centre Route) wannan dalilin ya jawo kafuwar Unguwanni a cikin Birnin Katsina, wanda bakin Yan Kasuwa daga Kasashen Larabawa da Azbin da Berbers da sauransu sukayi sanadiyyar Kafuwarsu, Misali Unguwar Sararin Tsako Dake cikin Birnin Katsina Buzayene daga Agades suka kafata a sanadiyyar Kasuwancin Sahara, Unguwar Yansiliyu Dake cikin Birnin Katsina Larabawan Afirika ne suka kafata da sauransu.
To haka itama Unguwar ALBABA Dake cikin Birnin Katsina Larabawan Afirika ne daga Kasar Algeria suka kafata. Unguwar ALBABA da Yansiliyi daga Gabas, daga kudu kuwa tayi iyaka da Unguwar Alkali. Daga Yamma, tayi iyaka da Rafin Dadi da Darma.
Ana kyautata zaton Unguwar ALBABA ta kafu tun wajen shekarar 1820, lokacin mulkin Sarkin Katsina Ummarun Dallaje. Tarihi ya nuna zuriyar wani babban Dan Kasuwane kuma Wakilin Kasuwanci Tsakanin Masarautar Katsina da kuma Kamfanin su Dake Tuat ta Kudancin Kasar Algeria. Shi dai wannan Dan Kasuwa cikakken sunan shi shine Ahmad Abu al-Ghaith Attawati ibn Sayyaid Mohammad Ahmad al-wajda, wanda aka Sani da Abulgaisu. Asalin shi Berber ne daga Tuat ta Kasar Algeria yazo Katsina a matsayin Wakilin Kasuwanci ( Trade Consul) Tsakanin Katsina da Kamfanin su Dake Algeria. Sai kuma aka sabka dashi a Unguwar ALBABA Dake cikin Birnin Katsina, wannan dalilin ne yasa Unguwar ta samu sunan ALBABA, watau Unguwar da Berbers suka zauna, watau Larabawan Afirika Dake Algeria.
Daya daga cikin manyan kayan da Abul Gaisu yake hudda Kasuwanci Tsakanin Katsina da Kasar shi Algeria itace ta bayi, ya kasance Yana sayen bayi daga Fadar Katsina da Daura da Hadejia, daga nanne zai loda su bisa Rakumma har zuwa Tuat ta Kasar Algeria. Tarihi ya nuna Abu al-Gaiths shine asalin kafuwar Garin Yan Rakumma Dake Ajiya ta Karamar Hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina ta yanzu, ance anan Yan Rakumma yake tara bayi bisa Rakumma kamin ya wuce dasu Kasar Algeria a wajen shekarar 1820, daga nanne aka sama Garin suna Yan Rakumma. Abul al-Gaiths ya kasance a matsayin Mai shiga huldar Kasuwanci Tsakanin bakin Larawa Yan Kasuwa a Birnin Katsina, wannan dalilin yasa ya samu karfuwa wajen Sarakunnan Dallazawa na Katsina musamman lokacin Ummarun Dallaje (1807-1835), Saddiqu (1835-1844) da Muhammadu Bello (1844-1870). Daga cikin Yayan Abul al-Gaiths a Katsina akwai Usman, Abdulkarim,Hafsat, Maryam Safiya da sauransu. Daga cikin Jikokin Abul Gaiths Dake Unguwar ALBABA akwai Mariganyi Alhaji Ibrahim Mai-dawa 1885-1965 da Hajiya Maryama Ibrahim Mai-dawa ( Yar baba) an haifeta acikin shekarar 1916. Har ya zuwa ya zu Gidan Ahmad Abu Al-Gaiths Yana nan a Unguwar ALBABA Dake cikin Birnin Katsina.
Haka nan kuma baya ga zuriyar Abu al-Gaiths Dake Unguwar ALBABA akwai kuma zuriyar Sarkin Larabawa Abba Almu, wadanda Suma Asalinsu Larabawan Afirika ne da suka zo Katsina a sanadiyyar Kasuwanci Sahara ( Transharan Trade) Daga cikin wannan zuriyar ne aka samu su Abba Dayyabu, da Abba Jaye, Sarkin Sharifai na yanzu.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.