Wata babbar kotun majistire da ke Sokoto a ranar Juma’a ta dage shari’ar Hamdiyya Sidi, wata matashiya mai amfani da kafafen sada zumunta da ake zargi da tayar da hankula a bainar jama’a, zuwa ranakun 13 da 14 ga watan Maris domin kare kanta.
Babban Alkalin kotun, Faruk Umar, ya yanke hukuncin dage shari’ar bayan da mai gabatar da kara, Insfekta Khalid Musa, ya gabatar da shaida daga jami’in bincike na ‘yan sanda kan shari’ar, Tukur Abdulhadi.
An gurfanar da Sidi mai shekaru 18 bisa zargin wallafa wani abu a dandalin sada zumunta da ka iya haddasa tashin hankali.
Ana zarginta da yin wani bidiyo da ke caccakar sakaci da hukumomi keyi, wajen magance matsalar ‘yan bindiga a Sabon Birnin Daji da wasu sassan jihar Sokoto.
A cewar takardar farko ta binciken ‘yan sanda, Sidi ta zargi cewa ‘yan bindiga na ci gaba da sace mutane tare da neman kudin fansa a wasu yankuna ba tare da daukar wani kwakkwaran mataki daga hukumomi ba.
A zaman farko da aka yi kan shari’ar, mai gabatar da kara ya bayyana cewa laifin ya saba wa dokar penal code, sai dai wacce ake tuhuma ta musanta zargin.
A ci gaba da sauraron shari’ar a ranar Juma’a, shaidar da aka gabatar ta bayyana cewa shi ne jami’in bincike wnada ya karbi bayanan wacce ake tuhuma.
Ya gabatar da wata na’urar ajiya (flash drive) da kuma fassarar bayanan da aka samu daga gare ta, wanda alkalin ya amince da su a matsayin shaida. A yayin tambayoyin da lauyan wacce ake kara, Mustapha Danjuma, ya yi wa shaidar, jami’in binciken ya amsa cewa an karbi bayanan wacce ake tuhuma ba tare da wakilcin lauyanta ba.
Ya kuma bayyana cewa an samu bidiyon ne daga kwamfutar tebur inda aka ajiye shi.
Alkalin kotun ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 13 da 14 ga watan Maris don ci gaba da shari’a, sannan ya umarci wacce ake kara da ta ci gaba da zama kan belin da aka ba ta a baya.
(NAN)