Lt. Col UK Bello: Jarumin da Ya Sadaukar da Rayuwarsa Don Shugabansa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21022025_072933_FB_IMG_1740122147299.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, Febrairu 21, 2025

Lt. Col Usman Kankada Bello ya kasance dogari mai aminci ga Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).

Ya kasance abokin aiki ga mafi yawancin sojojin da suka jagoranci juyin mulkin 1990, musamman wanda ya jagoranci juyin mulki, Gideon Orkar.

A lokacin da sojoji 'yan juyin mulkin suka shiga Dodan Barracks, UK Bello ya fuskance su, bai san cewa an riga an kashe duk wasu makaman fadar shugaban kasa ba…

An Kashe Makamai? Yaya Haka Ta Faru?

Kwanaki kafin a kai harin, daya daga cikin masu juyin mulkin wanda shi ne injiniyan soji mai kula da makamai ya ziyarci Dodan Barracks don yin "gyara da kula da kayan aiki". Ba tare da sanin Bello da IBB ba, mutumin ya riga ya sanya makaman fadar cikin rashin aiki kafin ya bar wurin.

Lokacin da aka fara harin, IBB ya tsere ta wata sirriyar hanya ta karkashin kasa kafin 'yan juyin mulki su cafke shi. Daga nan, ya bayyana a Obalende sannan ya nufi wani wuri da ba a sani ba, har sai da Sani Abacha da Raji Rasaki suka fatattaki 'yan juyin mulkin, suka kama su kuma suka mayar da mulki ga IBB.

Mutuwar Bello a Matsayin Jarumi

Yayin da UK Bello ya fuskanci 'yan juyin mulkin, Orkar ya yi dariya ya ce masa ya janye daga kokarin hana su cafke IBB. Orkar ba ya son kashe Bello saboda suna da kusanci, amma Bello ya ki cin amanar ubangidansa.

Bello ya gargadi 'yan juyin mulkin su janye, amma suka sake gargadinsa. Sai ya haura kan wata tankar yaki domin ya bude wuta – amma makamin ya ki aiki!

Da hakan ta faru, 'yan juyin mulkin suka rufe shi da harbin bindiga kamar ruwan sama, tare da sojojinsa. Bello ya mutu a matsayin jarumi mai aminci ga shugabansa.

Dole ne a tuna cewa kokarin Bello na kawo tsaiko ko jinkiri ga 'yan juyin mulki ya ba wa IBB damar gano hanyar da ya tsere ta karkashin kasa, saboda an yanke wutar barikin soji wurin yana cikin duhu.

22 ga Afrilu, 1990. Ina kake a wannan rana?

Follow Us