ZAMAN MU DA UMARU MUSA 'YAR'ADUA DA MD YUSUFU

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20022025_180837_Screenshot_20250220-190617.jpg


...Mutane ake kallo kafin cancanta a muƙami

...Kwangila ana iya ba kowa

...Muƙamin Abuja ana iya fifita cancanta

Daga Ɗanjuma Katsina

Wata rana MD Yusufu ya zo Katsina, sai ya ce zai je wajen Alhaji Ɗahiru Mangal domin ya yi masa godiya a kan yadda yake tallafa wa ɗaliban da mukan yaye a Katsina Vocational Training Centre.

Ya ce zai kuma je wajen Gwamna Malam Umaru Musa 'Yar'adua shi ma ya yi masa godiya a kan yadda gwamnatin Katsina take tallafa wa ɗaliban da mukan yaye.

Ya ce akwai kuma wani alƙawarin da ya ɗauko yana son ya cika shi.

Hussaini Dambo shi ne wanda ya samar mana lokaci da Gwamna Umaru Musa a ranar Asabar da dare.

Mun same shi a gida, muka shiga ɗakin da yake ganawa da mutane mu uku.

MD Yusuf ya ce wannan yaron shi ne ke kula da Cibiyar nan ta Katsina Vocational Training Centre, shi ya kawo shawarar kafa ta na ƙarfafa masa gwiwa.

MD Yusufu bayan ya yi godiya a kan irin yadda gwamnatin Katsina ke tafiya kafaɗa da kafaɗa da Cibiyar, sai ya ce yana da shawarwari guda biyu. 

Na farko, gwamnati ta kafa tata a sa mata suna, Katsina Reformatory Centre, inda ya yi bayanin yadda ya kamata ta kasance.

Na biyu, Katsina ta yi koyi da ƙasashen kudancin Afrika. Ya ce bayan kammala yaƙe- yaƙe sai suka ga matasa ga su nan zaune ba aiki, sai suka kakkafa Craft Villagers na horas da matasa sana'o'i.

Ya ce masu matsalar shaye-shaye, sai a kai su Reformatory Center, masu lafiyar su kuma a kai su Craft Village.

Nan take Umaru ya amsa duk. Ya ce insha Allah gwamnatin Katsina za ta yi.

MD Yusuf sai ya ce, "Alƙawari na uku da na ɗauko shi ne, wani ne wanda ya ce ka san shi, ya ce yana son a ba shi dama a gwamnatin Katsina shi ma ya ba da tasa gudunmuwar."

Umaru Musa ya ce, "Na san shi, amintacce ne, kuma jajirtacce. Ya ce, amma a tsarin siyasarmu sai dai mu yi ƙoƙarin samar masa gurbi a Abuja ya riƙe mana a can."

Malam Umar ya ce, "A muƙamin cikin gida ana son wanda ya san gidan, yake zaune da mutane. Ya san halayyarsu da ɗabi'unsu, zai iya haƙuri da halayyarsu, kuma wanda ya yi mana wahala a siyasance, ya san waɗanda suka yi wahala tare."

Malam Umaru ya ce a faɗa masa na yi alƙawarin zan nema masa da tsaya masa a Abuja, amma in an samu ya riƙa ziyartar gida yana caɗanya da mutane."

Umaru Musa ya ce muƙamin siyasa bayan cancanta, riƙon amana, ana kuma duba karɓuwar mutum ga daga inda za a ɗauko shi.

Ya ce, kwangila ana iya ba kowa bisa ƙwarewa da cancanta, amma muƙami ana ƙarawa da ko dai jama'arsa suka kawo shi, ko kuma in aka ba shi mutanensa za su yi farin ciki da ba shi da aka yi saboda ƙila yana hidimta masu.

Ya ƙara da cewa, "Baba (kamar yadda yake iran MD Yusuf), a muƙamin cikin gida mutanen da ya fito cikinsu muke kallo farko kafin sauran cancantar. Idan yana tare da mutanensa sai a ɗora daga nan," ya jaddada.

Allah ya jiƙan Malam Umaru, ya cika alƙawarinsa, don kuwa an samar wa mutumin muƙami har sai da ya yi maimaici sau biyu a bisa kujerar.

Allah ya jiƙan MD Yusuf, shi ma yanzu ya shekara tara da rasuwa, har ya bar duniya bai taɓa zuwa ko aike ba ga wanda ya yi wa ƙoƙarin, kamar yadda ya faɗa min da ya zo gaisuwar rasuwarsa.

Follow Us