Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 19th Febrairu 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da sabon Shirin Kiwon Awaki da nufin bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a. Wannan shiri, wanda aka kaddamar a ranar 17 ga Fabrairu, 2025, yana da burin farfado da kiwon awaki tare da amfani da fasahohin zamani don kara habaka fannin kiwo a jihar.
A yayin taron manema labarai da aka gudanar a Cibiyar ‘Yan Jarida da ke Fadar Gwamnatin Jihar Katsina a ranar Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025, Alhaji Yusuf Suleman Jibia, Mai Ba da Shawara na Musamman ga Gwamna kan Kiwon Dabbobi da Gandun Daji, ya bayyana cewa shirin yana da manyan matakai guda biyu da za su taimaka wajen habaka kiwo a jihar.
Shirin yana da mataki biyu kamar yadda ya yi karin haske: Mataki na farko na shirin yana mayar da hankali kan karfafawa mata gwiwa ta hanyar raba musu awaki. A kowace gunduma 361 da ke jihar Katsina, mata goma za su amfana da awaki hudu—uku mata da namiji guda. Bugu da kari, kowacce mace za ta sami buhun tallafi da ya kunshi Dusar alkama da gishirin awaki.
A kowace gunduma, za a zaɓi manomi guda da ke da sha’awar kiwon dabobbi domin ba shi awaki 50—namiji 10 da mata 40, tare da kayan tallafi don bunkasa kiwo a manyan gonaki.
Gwamnati ta kafa cibiyoyin killace dabbobi uku a Dannakola, Ladanawa, da Kabomo don tabbatar da lafiyar awakin kafin a mika su ga manoman da suka cancanta.
A bangare na biyu na shirin shi ne kafa babbar gona ta kiwon awaki a Cibiyar Ladanawa Farm, inda za a samar da awaki 3,000—dukkan su mata—domin haihuwa ta hanyar amfani da maniyyin awaki masu inganci daga ketare. Wannan zai taimaka wajen bunkasa jinsin awakin da ake kiwo a jihar Katsina.
An ware hektare 70 na fili domin shuka makiyaya na musamman da za su samar da ingantacciyar ciyawa ga dabbobin da ke gonar Ladanawa.
Shirin zai kasance a karkashin kulawar kwararru da za su rika kiwon awakin, ba su kulawar lafiya, da kuma sarrafa su har na tsawon shekara guda, kafin daga bisani a mika su ga Ma’aikatar Kiwon Dabbobi da Gandun Daji don ci gaba da gudanar da shirin.
An ware kimanin Naira biliyan 5 don aiwatar da wannan shiri. Sai dai, Alhaji Yusuf Suleman Jibia ya bayyana cewa kudaden ba dole ne a kashe su gaba daya ba, domin za a bi matakan da za su tabbatar da ingantaccen gudanarwa da tsawaita shirin cikin nasara.
Gwamnatin Jihar Katsina na da burin inganta harkokin noma da kiwo, tare da habaka tsaron abinci da bunkasa tattalin arzikin jama’a
Alhaji Yusuf Suleman Jibia ya jaddada cewa wannan shirin ba wai kawai zai tallafawa manoma da masu kiwo ba, har ma zai samar da ayyukan yi, bunkasa kasuwanci, da kuma kawo sauyi a fannin kiwon awaki a jihar.
Gwamnatin Jihar Katsina tana da kwarin gwiwar cewa wannan shiri zai haifar da gagarumin ci gaba ga manoma da ‘yan kasuwa, kuma zai mayar da kiwon awaki wani muhimmin ginshiki na tattalin arzikin jihar.