Katsina Times
A kalla mutane bakwai, ciki har da 'Yan gida daya, sun rasa rayukansu a wani harin ta sama da aka kai a kauyen Yauni da ke gundumar Zakka a karamar hukumar Safana, Jihar Katsina, a ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa, kafin faruwar wannan lamari, wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro uku, ciki har da ‘yan sanda biyu da kuma wani jami’in Kungiyar Tsaron Al’umma ta Jihar Katsina (CWC), yayin da suke fafatawa da miyagun.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, wannan tashin hankali ya samo asali ne daga zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar, inda aka samu bayanan sirri cewa ‘yan bindiga na shirin kai hari kan masu kada kuri’a a Zakka.
Bayan samun wannan bayani, jami’an tsaro sun garzaya domin dakile farmakin, wanda ya janyo musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindigar. A yayin artabun, wani dan sanda da jami’in CWC sun mutu nan take, yayin da wani dan sanda na uku da ya jikkata daga bisani ya rasu.
Majiyar ta bayyana cewa, bayan wannan artabu, wani jirgin yaki da ake kyautata zaton na rundunar soji ne, ya dira domin taimakawa, amma sai ya jefa bam a kauyen Yauni da ke kudancin Zakka, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane shida daga gida daya, yayin da wata mata ta samu raunuka.
Wannan ba shi ne karon farko da al’ummar yankin ke fuskantar irin wannan hari daga sama ba. A watan Yuli na shekarar 2022, wani jirgin yaki ya jefa bam a kauyen Kunkunni da ke karamar hukumar Safana, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu tara.
Duk kokarin jin ta bakin ‘yan sanda da sojoji kan wannan lamarin ya ci tura. Sai dai rahoton Deutsche Welle na Jamus ya ruwaito wasu shaidu na tabbatar da aukuwar harin.