Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina (KTSIEC) ta fitar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar 15 ga Fabrairu, 2025, inda jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe dukkan kujerun da aka fafata a kai.
Tattara sakamakon ya samu jinkiri sakamakon wasu matsaloli a yankuna daban-daban, lamarin da ya hana fitar da sakamakon nan take. Zuwa ƙarfe 12 na dare bayan ranar zaɓe, an samu sakamakon ƙananan hukumomi 24 kacal daga cikin 34. Sauran ƙananan hukumomi 10—Batsari, Charanchi, Dandume, Daura, Funtua, Kankia, Katsina, Mani, Dutsinma, da Sabuwa—sun mika nasu ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Fabrairu.
A cewar sakamakon ƙarshe da KTSIEC ta fitar, jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 34 tare da kujerun kansiloli, inda babu wata jam’iyya da ta samu nasara. Jam’iyyun da suka shiga takarar sun hada da Accord (A), African Action Congress (AAC), African Development Congress (ADC), da Boot Party (BP).
Bayan bayyana sakamakon, KTSIEC ta gode wa jama’ar Jihar Katsina bisa hadin kai da goyon bayan da suka bayar, musamman masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe, wanda ya taimaka wajen gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.
A yayin wani taron manema labarai da kungiyar Inter-Party Advisory Council (IPAC) ta kira a Katsina a ranar Lahadi, 16 ga watan Fabrairu, shugaban kungiyar, Alhaji Salimu Lawal Boyi, ya jinjinawa hukumar KTSIEC bisa gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana.
Ya kuma yaba da ƙoƙarin dukkan ‘yan takarar da suka fafata a zaɓen, inda ya shawarci wadanda ba su samu nasara ba da kada su karaya, amma su shirya tsaf domin zaɓe na gaba.
Daga karshe, Boyi ya taya wadanda suka yi nasara murna tare da yin kira ga ‘yan siyasa da su hada kai domin ci gaban jihar.