BINCIKEN MUSAMMAN : A INA AKE TSARE DA JANAR MAHARAZU TSIGA? SUWA SUKA SACE SHI!!?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14022025_160942_image-108.png

Muazu Hassan I Katsina times 

Jaridun Katsina times sun yi binciken ya aka dauke janaral tsiga a garinsu na tsiga?su wa suka sace shi? A   binciken namu munyi magana da mutane daban daban kuma, zamu kawo rahotonni aka  lamarin.

INA AKE TSARE DA TSIGA?

A binciken mu mun samu zantawa da wasu da aka sato daga garin kandarawa ta karamar hukumar Bakori a ranar 14/1/2025 aka tsare su, sai da aka biya kudin fansa.cikin su har da mata da yara kanana 
Bayan hada kudi Naira milyan talatin aka kaima Barayin na daji  sannan suka sako su a ranar talatar da ta wuce.

Wadannan tsararrun da aka sako sun fada "yan uwansu ciki har da jaridun Katsina time cewa, suna can inda ake tsare dasu  aka kawo janaral Maharazu tsiga.

Sun tabbatar da sun ganshi ido da ido, suka kara da cewa barayin na kula dashi sosai, Hatta ruwan sha na roba suke bashi.
Sukace sunji barayin na fadin cewa basu son abin da zai same shi na rashin lafiya a wajensu.

A INA AKE TSARE DASHI?

Tsararrun da aka sako sun ce a dajin Bununu dake karamar hukumar faskari iyaka da karamar hukumar kankara.A wannan dajin  aka kaisu sukayi zaman da sai da aka biya kudin fansa suka sako su.
Suka ce, suna can aka kai janar Maharasu Tsiga kuma acan suka baro shi.

WACE DABA CE TA DAUKE SHI?

Binciken mu, ana tsammanin hari na hada ka ne.Amma wanda ake zargi mai karfi shine , sanannen dan ta addar nan  dake karamar hukumar kankara, yankin zango mai suna  Babaro ana zargin yana da hannu dumu dumu in ma bashi bane kanwa uwar gami.
Babaro, barawon daji ne da ya dau shekaru yana barnarsa a yankin kankara wani lokaci ya shiga zamfara ,wani lokacin yankin faskari.yana da yara da makamai masu yawa a tare dashi.

Ya taba ikirarin amsar tuba har ma aka rika muamala dashi.A daminar da ta gabata ya sanya ma gonaki haraji duk wadanda suka biya, ya kyale su sunyi nomansu.
Akwai zargi da bamu tabbatar dashi ba shine,kusan duk abin da akan rabar a karamar hukumar kankara, ana aika masa ya raba ma  talakkawan dake karkashin shi.
Munyi kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar   kankara mai barin gado akan wannan zargin,amma bamu samu ba.A waya da sakon hannu da kokarin ganin shi ido da ido.

Wani binciken ya nuna akwai hannun wani dan ta adda dake da karfi a yankin faskari wanda ake ma lakabi da "Raba aiki" wanda yake,kane ne ga Adamu Aleru.

Katsina times 
@ www.katsinatimes.com 
Jaridar Taskar labarai 
@ www.taskarlabarai.com 
The links news
@ www.thelinks news.com
All in All social media handles

Follow Us