Zaharaddeen Ishaq Abubakar I Katsina Times
KATSINA – A wasan karshe na gasar Isah Miqdad AD Saude Unity Cup, Durbi Strikers sun samu nasara a kan Kangiwa bayan bugun fenariti mai cike da rikici, inda suka doke su da ci 5-4 a ranar Alhamis, 13 ga Fabrairu, 2025.
Wasan karshe da aka gudanar a Katsina ya nuna bajintar kungiyoyin biyu, yayin da suka fafata da karfin gwiwa domin lashe kofin. Bayan tashi wasan daidai, dole aka je bugun fenariti, inda Durbi Strikers suka nuna kwarewa da kwanciyar hankali wajen cin kwallaye.
Gasar ta jawo kungiyoyin kwallon kafa da dama daga sassa daban-daban na Katsina, lamarin da ya nuna irin sha’awar da ake da ita ga wasan kwallon kafa a yankin. Kungiyoyin sun nuna kwarewa da kyakkyawar wasanni, wanda ya sanya gasar ta kasance abin sha’awa ga masoya da masu ruwa da tsaki.
Manyan baki daga bangarori daban-daban sun halarta domin kara daraja gasar. Daga cikin wadanda suka halarci wasan karshe akwai dan takarar shugaban karamar hukumar Katsina, Hon. Isa Miqdad tare da mataimakinsa, Hon. Saulawa. Haka nan akwai Hon. Sani Aliyu Danlami, dan majalisar tarayya; Hon. Aliyu Abubakar Albaba, dan majalisar dokokin jihar Katsina; shugaban kungiyar dillalan man fetur ta jihar, Alhaji Aminu Wali; da tsohon shugaban kasuwar Katsina, Alhaji Abbas Labaran Albaba. Wasan ya jawo hankalin matasa maza da mata, tare da masoya kwallon kafa daga sassa daban-daban na al'umma.
Gasar Isah Miqdad AD Saude Unity Cup ta zama wata muhimmiyar dama ga matasan ‘yan wasa a Katsina, inda take basu zarafin nuna kwarewarsu da samun gogewa a wasanni. Masu shirya gasar sun bayyana kudirinsu na ci gaba da habaka wannan gasa a nan gaba domin bunkasa kwallon kafa daga tushe a yankin.
Da wannan nasara, Durbi Strikers sun tabbatar da kansu a matsayin daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a yankin, kuma wannan nasara za ta ci gaba da zaburar da matasa masu sha’awar wasan kwallon kafa domin kokarin cimma gagarumar nasara a fagen wasanni.