Jagorancin Sabbin shugabannin IPMAN Zai Kara Saukaka Sayar da Man Fetur -Wali

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13022025_193703_FB_IMG_1739475339467.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar I Katsina Times

Sabon shugaban kungiyar dillalan man fetur na jihar Katsina (IPMAN), Aminu Ahmad Wali mai Kamfanin A.A Rahamawa, ya bayyana cewa jihar Katsina ce ke kan gaba wajen saukaka sayar da man fetur a Najeriya.  

A.A Rahamawa ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis, 13 ga Fabrairu, 2025, yayin bikin rantsar da sabbin shugabannin IPMAN na jihar Katsina, wanda aka gudanar a dakin taro na Aldusar, cikin birnin Katsina.  

A yayin jawabinsa, Rahamawa ya bayyana cewa nasarar da ake samu wajen wadatar da mai a jihar Katsina na da nasaba da kyakkyawan tsarin da kungiyar ke aiwatarwa domin amfanin al’umma. Ya jaddada cewa akwai ‘yan kasuwa da ke yin kasuwanci cikin gaskiya da rikon amana, ba don riba kadai ba, sai don kyautata wa al’ummar jihar Katsina duba da halin da ake ciki.  

Ya kuma yi alkawarin kawo gagarumin ci gaba ga kungiyar a karkashin jagorancinsa, tare da tabbatar da ingantacciyar tafiya da za ta kara bunkasa harkar dillancin man fetur a jihar.  

A karshe, Rahamawa ya yi kira ga gwamnati da ta samar wa kungiyar wata sakatariya domin saukaka ayyukan da za su taimaka wajen zamanantar da kasuwancin man fetur a jihar.  

Bikin rantsarwar ya samu halartar fitattun mutane daga bangarori daban-daban, ciki har da wakilin shugaban IPMAN na kasa, Hannafi Aminu, tsohon shugaban IPMAN na jihar Katsina, Abbas Sani Hamza Mai Goro, da shugaban rukunin Danmarna Petroleum, Alhaji Dahiru Usman Sarki. Haka nan, wakilan hukumomi da suka hada da ‘yan sanda da hukumar hana fasa kwabri suma sun halarci taron, tare da sauran manyan baki daga ciki da wajen jihar.

Follow Us