Hukumar Zabe Ta Katsina Ta Fara Raba Kayayyakin Zaben Kananan Hukumomi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13022025_184700_FB_IMG_1739472299483.jpg



Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times

Hukumar Zabe ta Jihar Katsina ta kaddamar da rarraba muhimman kayayyakin da za a yi amfani da su a zaben kananan hukumomi da ke tafe, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga Fabrairu, 2025.  

Shugaban hukumar, Alhaji Lawal Alasan Faskari, ne ya jagoranci kaddamar da rabon kayayyakin a ranar Alhamis, 13 ga Fabrairu, 2025, a hedkwatar hukumar da ke kan titin tsohuwar fadar gwamnatin jihar.  

A yayin taron, Faskari ya bayyana cewa kayan za a raba su ne ga dukkan kananan hukumomi 34 da ke Katsina, rumfunan zabe 6,652 da mazabu 361 da ake gudanar da zaben kansiloli.  

Ya kuma bayyana cewa kayayyakin da za a yi amfani da su a wannan karo sun bambanta da na baya, domin an sanya sunan kowace karamar hukuma a jikin kowanne kaya don tabbatar da ingantaccen tsari da kaucewa matsaloli a lokacin zabe.

Follow Us