Gidauniyar 'Dangiwa Literary Foundation' ta kaddamar da Littafi da karrama marubuta.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13022025_183138_FB_IMG_1739471410470.jpg


Auwal Isah Musa (Katsina Times)

Shahararriyar gidauniyar nan ta Ministan Gidaje da Raya Birane, 'Arc. Ahmed Musa Dangiwa Literary Foundation', ta kaddamar da littafi tare da karrama wadanda suka yi zarra a gasar rubutun 'Gajerun Labaran Hausa' wanda gidauniyar ta shirya cikin shekaru biyu da suka gabata.

Littafin mai taken "Burina", an kaddamar da shi ne a ranar Alhamis din nan 13 ga Fabrairun 2025, a dakin taro na Kabir Aliyu Maska da ke hukumar ma'aikatan kananan hukumomi na jihar Katsina.

Gasar rubutun wadda ke zuwa a karo na uku, ta samu shigowar mutane 32 daga mabambantan jihohin arewacin Nijeriya, a yayin da mutane 16 daga cikinsu suka samu nasarar tsallakewa zuwa zagayen karshe na gasar.

Da yake jawabi a taron, shugaban gidauniyar, Arc. Ahmed Musa Dangiwa ya yaba wa wadanda suka shiga gasar tare da jinjina masu bisa ga dogon nazari, bincike gami da hazakar da kowanensu ya nuna a cikin gasar.

A nasa jawabin a matsayinsa na babban bako a taron, gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Honorabul Faruq Lawal Jobe, ya shawarci gidauniyar da ta taskace fikirorin marubutan duk da cewar su ne aka tattara aka yi littafin, inda ya bayyana rubututtukan nasu a matsayin masu amfani ga al'ummarmu ta bangarorin addini, al'adu da zamantakewarta na rayuwar yau da kullum.

Wadanda suka lashe gasar a matakai na daya, biyu da uku sun hada da: Abu Ubaida Sani/Aisha Muhammad Bazango daga jihar Bauchi a matsayin wadanda suka zo na daya, sai Firdausi Muhammad Sodangi daga jihar Katsina wadda ta zo na biyu, shi kuma Lawal Muhammad PRP daga jihar Kano wanda ya zo na uku.

An bayyana kyautar Naira dubu 400,000 ga mutum biyu da suka zo na daya, da Naira 300,000 ga wadda ta zo na biyu, sai kuma wanda ya zo na uku da kyautar Naira 200,000. Haka zalika, an kara masu da wasu kyaututtuka da suka hada da shaidar shiga gasar, alluna da kuma wani adadi na littafin da aka kaddamar a wajen.

Sauran wadanda suka shiga gasar kuwa, an ba su tukuicin Naira dubu 50,000 ga kowannensu, tare da karin wasu kyaututtuka.

Wadanda da suka gabatar da Makaloli a taron sun hada da: Alkalin alkalai na jihar Katsina, Justice Musa Da ladi Abubakar wanda ya samu wakilcin Dr. Aliyu Idris Funtua, Shugaban hukumar gudanarwa na makarantar kwalejin nazarin kimiyyar zamani, kirkire-kirkire da harkokin shugabanci, Injiniya Muttaka Rabe Darma, da Kwamared Alhaji Dr. Bilya Sanda.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da: Farfesa Sani Audu Fari, Farfesa Lawal Aminu Auta (BUK), Dr. Bashir Abu Sabe, Alhaji Muhammadu Magaji Abubakar, Alhaji Kabir Mai kwai, Barista Murtala Aliyu Kankiya, Malam Naufal Ahmad, Alhaji Ibrahim Ali Guguwa, Injiniya Mustapha Ibrahim Ruma da sauransu.

Follow Us