Dan takarar kujerar shugabancin Karamar Hukumar Safana, Abdullahi Sani Brazil, ya karɓi goyon bayan manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a taron yakin neman zabensa da aka gudanar a garin Safana.
Taron, wanda ya samu halartar fitattun shugabanni da masu ruwa da tsaki a siyasar yankin, ya gudana ne domin tallafa wa dan takarar da tattauna hanyoyin samun nasara a babban zabe mai zuwa. Cikin wadanda suka halarta akwai APC Legal Adviser, Iliya Runka; Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Hon. Abduljalal Haruna; wakilan majalisar jiha da na tarayya irin su Hon. Abdulkadir Zakka da Hon. Abbah Dayyabu; da kuma SSA Public Engagement, Yusuf Ibrahim.
Sauran fitattun ‘yan siyasa da suka halarci taron sun hada da SA C Watch, Shafiu Rabiu Safana; Engineer Aminu Dayyabu Safana; Alhaji Sada Zakka; da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar.
A yayin taron, Abdullahi Sani Brazil ya gode wa shugabannin jam’iyyar da magoya bayansa bisa goyon bayan da suke ba shi, yana mai jaddada aniyarsa ta kawo ci gaba da inganta rayuwar al’ummar Safana idan aka zabesa. Ya bayyana cewa, idan ya samu nasara, zai mayar da hankali kan inganta harkokin noma, kiwon lafiya, da ilimi, tare da bunkasa tsaro a yankin.
Jiga-jigan jam’iyyar da suka yi jawabi a wurin sun yabawa shirin dan takarar, tare da bukatar jama’a su ci gaba da mara masa baya domin samun shugabanci nagari a karamar hukumar Safana.
Taron ya gudana cikin nasara, inda aka bayyana shirin ci gaba da kamfen a mazabu daban-daban na yankin kafin ranar zabe.