Nijerya na Fuskantar Barazanar Rashin Damar Aikin Hajjin bana, 2025

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes10022025_160919_Hajj.jpg


Katsina Times 

Kungiyar Shugabannin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi ta bayyana damuwa kan yiyuwar ‘yan Najeriya su kasa halartar Hajjin 2025 bayan da ake zargin Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta soke kwantiragi da wani kamfani a Saudiyya.  

A ranar 17 ga watan Janairu, NAHCON ta kulla yarjejeniya da kamfanin Mashariq Al-Dhahabiah na Saudiyya, wanda ke da alhakin samar da abinci da masauki ga alhazai ‘yan Najeriya a ƙasar mai tsarki. Sai dai, sakataren kungiyar, Abubakar Salihu, ya ce soke kwantiragin na iya hana alhazai samun bizar shiga Saudiyya domin Hajjin 2025.  

Da aka tambayi NAHCON kan lamarin, hukumar ta musanta zargin, tana mai bayyana shi a matsayin jita-jita. Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ta bakin kakakin NAHCON, Muhammed Ahmed Musa, ya ce, "Mutane na ta yin hasashe kan abin da muka je Saudiyya muka yi, amma da zarar an kammala tsarin, za mu sanar da manema labarai."  

Duk da wannan karin haske daga NAHCON, Salihu ya dage cewa idan aka samu matsala wajen halartar Hajjin 2025, to dole a ɗora laifin kan hukumar. Ya nuna takaicinsa cewa bayan an gudanar da tsari mai tsauri na zaɓen kamfanin da kuma sanya hannu kan kwangilar Mashair da Mashariq Al-Dhahabiah, shugaban NAHCON ya soke kwangilar ta hanyar dandalin lantarkin yanar gizo.

A gefe guda, kungiyar Independent Hajj Reporters (IHR), wata ƙungiyar rajin kare hakkin alhazai, ta bukaci NAHCON da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi su daidaita sabanin da ke tsakaninsu domin tabbatar da ingantaccen shirin Hajjin 2025.  

A cikin wata sanarwa da mai kula da ita a ƙasa, Ibrahim Mohammed, ya sanya wa hannu, IHR ta gargadi cewa rashin warware sabanin da ke tsakanin NAHCON da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi kan zaɓen mai bada hidima ka iya kawo cikas ga shirin Hajjin 2025.

Follow Us