Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Reshen Katsina na Kungiyar Shugabannin Hukumomin Kananan Hukumomi a Najeriya (FOHOLGAN) ya shirya bikin bankwana domin girmama Shugaban Kungiyar na ƙasa, Malam Abdulrahman Marafa.
An gudanar da taron ne a ranar Lahadi, 9 ga Fabrairu, 2025, a dakin taro na Medical Health Workers Union, Kabir Usman Road, G.R.A, Katsina. Wannan biki ya zama wata dama ta nuna godiya da yabo ga Marafa bisa jagoranci nagari da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban FOHOLGAN, daidai da kammala wa’adin sa a aikin gwamnati.
Manyan baki, jami’an gwamnati, da mahukunta a harkar shugabancin kananan hukumomi sun halarci taron, inda suka jinjina wa kokarin Marafa wajen ƙarfafa tsarin mulkin kananan hukumomi, inganta gaskiya da rikon amana. Wadanda suka yi magana a wajen taron sun bayyana shi a matsayin shugaba nagari mai hangen nesa, wanda ya sadaukar da kansa domin inganta shugabanci da kyautata ayyuka a matakin kananan hukumomi.
Bikin ya kuma zama dama ta karrama tsofaffin Sakatarori na dindindin da suka yi ritaya a jihar Katsina, tare da nuna girmamawa ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, da Mataimakinsa, Faruq Lawal Jobe, bisa irin namijin kokarinsu a tafiyar da mulki.
Manyan baki sun yi ta bayyana irin kyawawan halaye da nagartar Abdulrahman Marafa. Daga cikin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu akwai Iyan Katsina, Shugaban Ma’aikatan Jihar Katsina, da Alhaji Mas’udu Almu Banye, wanda ke da kusanci da wanda aka shirya taron domin sa. Haka nan, Shugaban Karamar Hukumar Charanchi, wanda ya wakilci Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON), Injiniya Bello Yandaki, shi ma ya halarta, wanda shi ne Shugaban Karamar Hukumar Kaita.
Taron ya kasance cike da zumunci, yabo, da godiya, inda mahalarta suka bayyana Marafa a matsayin shugaba mai dattako, wanda gudunmawar da ya bayar a harkar shugabancin kananan hukumomi za ta ci gaba da zama abin koyi har tsawon lokaci.