Muhammad Ali Hafiziy, Katsina Times
Kungiyar Struggle For Good Governance ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin Farfesa Usman Yusuf, wanda Hukumar EFCC ta kama a Abuja.
Shugaban kungiyar, Comrade Habibu Ruma, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da suka gudanar a ofishinsu da ke Katsina, a ranar Asabar, 8 ga Janairu, 2025.
Da yake jawabi, Ruma ya ce kama Farfesa Usman Yusuf da kuma ci gaba da tsare shi, alama ce ta yadda gwamnati ke amfani da hanyoyi daban-daban wajen murƙushe 'yan adawa, musamman masu sukar manufofinta. Ya kara da cewa, ci gaba da tsare shi ba tare da wata hujja ta doka ba, na nuna cewa ana ƙoƙarin hana shi ci gaba da wayar da kan al'umma kan abubuwan da ke faruwa a kasa.
Shi ma Comrade Usman Hussaini Rafukka, ya nuna damuwarsa kan kama Farfesa Usman Yusuf, inda ya ce ba wai suna ƙalubalantar gwamnati ba ne, sai dai suna bukatar adalci. Ya yi nuni da cewa, binciken da kungiyarsu ta gudanar ya nuna cewa kamun bita da kulli ne kawai, ba bisa ƙa'ida aka yi shi ba.
Rafukka ya kuma yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na amfani da kama 'yan gwagwarmaya irin su Mahadi Shehu da Farfesa Usman Yusuf a matsayin hanyar tauye musu 'yanci. Ya ce irin wannan mataki na iya haifar da rashin zaman lafiya, musamman tsakanin matasa.
A ƙarshe, kungiyar ta sake yin kira ga gwamnatin Tinubu da ta gaggauta sakin Farfesa Usman Yusuf tare da ba shi haƙuri, domin ya koma cikin iyalansa lafiya.