Kungiyar Network for Good Governance and Transparency (NGGT) ta karrama wasu manyan jiga-jigai a Jihar Katsina bisa gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban al'umma. Taron karramawar, wanda aka gudanar a dakin taro na Katsina State Secretariat Complex, ya samu halartar manyan baki ciki har da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, da Darakta Janar na Hukumar KASSAROTA, Major Garba Yahya Rimi (Rtd.), wanda kuma shi ne Tafidan Kauran Katsina, tare da wasu fitattun mutane daga fadin jihar.
Kungiyar NGGT ta karrama Daraktan KASSAROTA, Major Garba Yahya Rimi, bisa kokarin da yake yi wajen habaka ci gaban matasa da kuma inganta ayyukan hukumar KASSAROTA a jihar. Haka nan, wasu daga cikin jami'an da suka goyi bayan wannan karramawa sun hada da ASTC A. Muntari, Kwamandan NGGT na shiyyar Katsina, da kuma jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Marwana Kofar Sauri.
Abubakar Marwana Kofar Sauri
Fans
Fans
Fans
Fans