Karamar Hukumar Zango Ta Tallafa wa Mata 252

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes04022025_130518_FB_IMG_1738669814055.jpg

Kimanin mata 252 ne duka samu tallafi na jari da kayan sana'a daga Karamar Hukumar Zango ta Jihar Katsina a cikin shekaru biyu.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Aminu Babangida Yardage ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da 'yan jarida a ofishinsa da ke Zango.

Ya ce matan tallafi da suka hada da wake, da kekunan dinki, da awaki da kuma tsabar kudi don su kama sana'o'i daban daban.

“A cikin wadannan matan su 252 da mukaminsa tallafa wa, mun zabo mata hamsin, muka ba su kekunan dinki da tallafin kudi domin su fara sana’ar dinki.

"Mun kuma ba wasu tiya goma-goma na wake domin su fara sana'ar awara, kuma muna sa ido a kansu, mun lura sun samu nasara a wannan sana’ar.

“Mun kuma raba ma wasu awaki, kowace mace ta samu awaki hudu, Nan da nan waɗannan awaking zasu hayayyafa, sai ku ga matan sun samu kudin da zasu rika jujjuya wa.

"Mata suna da rauni kuma duk abin da aka ba su, sun san yadda za su sarrafa shi don taimaka wa 'ya'yansu da mazajensu, yawancin matan da muka tallafawa sun yi nasara kwarai wajen kafaru sana'o'i" in ji Yardage.

Dangane da samar da tsaro a kan iyaka tsakanin karamar hukumar Zango da jamhuriyar Nijar mai tsawon kilomita 70, shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata majalisar ta hada hannu da hukumar kwastam, hukumar shige da fice da kuma 'yan sanda wajen kare kan iyakar.

Ya ce sun horar da kungiyoyin sa-kai na samar da tsaro kuma sun samar musu na'urar salula na walkie-talkie domin inganta sanarwa tsakaninsu da jami'an tsaro domin takaita miyagun laifuka a kan iyakokin.

“Mun horar da kungiyoyin ‘yan banga tare da samar musu da na'urar Walkie Talkie guda 75 domin inganta sadarwa wajen same da tsaro a kan iyaka.

“A kullum wadannan ‘yan bangan na gudanar da sintiri a kan iyakokin da kuma cikin manyan garuruwanmu don dakile shaye-shayen miyagun kwayoyi da daba da fyade.

"Cikin shekaru biyun nan mun ga an samu raguwar wadannan laifukan a Zango da kewaye,” inji Alhaji Babangida Yardage.

Ya kuma mika godiyarsa ga Gwamna Dikko Radda kan yadda ake ci gaba da fadadawa tare da gyare-gyaren makarantu da asibitoci a karamar hukumar.

Ya bayyana cewa a karon farko an ware naira miliyan 450 domin gudanar da aikin fadada babban asibitin garin Zango amma za a kara yawan kudin saboda hauhawar farashin kayan gini.

Shugaban karamar hukumar ya ce ya zuwa yanzu an kashe Naira miliyan 200 wajen biyan diyya ga masu gidaje da filaye da fadada asibitin zai shafa.

Ya yi nuni da cewa an biya diyya ga masu filiaye da gidaje 45 da ke kusa da asibitin da suka hada da masu gidaje 32 da masu fili 13.

Ya ce gwamnatin karamar hukumar ta kuma gudanar da wasu ayyukan tituna a karamar hukumar da suka hada da titin Zango zuwa Garni wanda ake kan aikinsa a hakkin yanzu.

Follow Us