Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kungiyar Cigaban Unguwar Yar’adua a Karamar Hukumar Katsina, Jihar Katsina, ta yi kira ga hukumomi da su gaggauta sakin Farfesa Usman Yusuf, wanda ke tsare na tsawon kwanaki, Kungiyar ta ce an kitsa zargin da ake yi masa ne don a hana shi fadin gaskiya kan manufofin gwamnati.
A yayin taron manema labarai, shugaban kungiyar ya nuna damuwa matuka kan ci gaba da tsare Farfesa Yusuf, yana mai cewa "wannan yunkuri ne na murkushe masu adawa da manufofin gwamnati." Ya bayyana cewa an zarge shi da ba da kwangila ga dan uwansa ba tare da kasafi ba, amma kungiyar ta ce ba a gabatar da wata kwakkwarar hujja ba da ke tabbatar da hakan.
"Farfesa Usman Yusuf yana fuskantar danniya ne kawai saboda yana amfani da yancin sa na fadin albarkacin baki, yana neman a kyautata shugabanci," in ji shugaban kungiyar.
Farfesa Usman Yusuf, wanda ya taba zama Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), ya dade yana sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yana mai cewa manufofin su sun haddasa matsaloli ga talakawa.
Daga cikin batutuwan da ya fi mayar da hankali akai sun hada da:
1. Wahalhalun Tattalin Arziki: Ya soki cire tallafin fetur da rage darajar naira, yana mai cewa hakan ya haddasa hauhawar farashi da karancin kudin shiga.
2. Sabon Tsarin Haraji: Ya bayyana cewa sabuwar manufar rarraba VAT da gwamnati ta kawo barazana ce ga hadin kan kasa, yana mai cewa mafi yawan talakawa ne za su fi shan wahala.
3. Almubazzaranci: Ya soki yadda gwamnati ke kashe kudade a kan abin da ba dole ba, musamman siyan sabon jirgin Shugaban Kasa, a daidai lokacin da miliyoyin ’yan Najeriya ke cikin kunci.
4. Murkushe ‘Yan Adawa: Ya soki yadda gwamnati ke hana masu adawa da ita fadin ra’ayinsu da gudanar da zanga-zanga, yana mai gargadin cewa hakan zai iya jefa kasar cikin mulkin kama karya.
5. Bada Hankali Kan Kasashen Waje: Ya bukaci gwamnati da ta fi mai da hankali kan rayuwar ‘yan Najeriya maimakon kashe kudade wajen tallafawa kungiyoyin kasa da kasa kamar ECOWAS.
Kungiyar Cigaban Unguwar Yar’adua ta lissafo manyan bukatunta kamar haka:
1. A saki Farfesa Usman Yusuf nan take: Kungiyar ta ce "ba wata doka da ta halasta ci gaba da tsare shi, don haka ya kamata a bar kotu ta yi aikinta.
2. A kawo karshen danniyar masu adawa: Kungiyar ta bukaci gwamnati da ta daina amfani da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa don murkushe wadanda ke sukar mulkin ta
3. Cin gashin kai ga bangaren shari’a:bSun yi kira ga kotuna da su daina barin manyan ‘yan siyasa su tsoma baki a shari’a domin cimma muradun su.
Kungiyar ta jaddada cewa wannan ba batun Farfesa Usman Yusuf kadai ba ne, illa kuwa gwagwarmaya ce don tabbatar da ‘yancin fadin albarkacin baki ga dukkan ‘yan Najeriya.
"Idan aka ci gaba da wannan rashin adalci," in ji kungiyar, "za a kai ga matakin da duk wanda ya soki gwamnati za a kitsa masa sharri, a tsare shi, ko a hana shi fadin ra’ayi."
A karshe, kungiyar ta yi kira ga kungiyoyin farar hula, masu fafutuka da al’umma baki daya da su mara mata baya wajen neman adalci ga Farfesa Usman Yusuf.