Isah Miqdad Ya Kaddamar da Taron Neman Goyon Baya Daga Shugabannin APC Na Mazabu a Katsina

top-news


Muhammad Ali Hafizy, @Katsina Times 

A ranar Juma’a, 31 ga watan Janairu 2025, ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya kaddamar da wata muhimmiya ganawa da shugabannin jam’iyyar a matakin mazabu. Wannan taron ya kasance wani bangare na shirin yakin neman zaɓensa, yayin da aka shiga matakin ƙarshe na shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da ke tafe cikin sati biyu.  

Hon. Isah Miqdad ya fara ganawarsa ne da shugabannin jam’iyyar na mazabu biyar daga cikin goma sha biyu da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Katsina. Mazabun da suka fara cin gajiyar wannan tattaunawa sun haɗa da Wakilin Kudu I, Wakilin Kudu II, Wakilin Kudu III, Wakilin Yamma I, da Wakilin Yamma II.  

A yayin ganawar, Hon. Miqdad ya gabatar da muhimman tsare-tsaren da ya tanadar domin ci gaban ƙaramar hukumar Katsina, inda ya jaddada kudurinsa na kawo sauye-sauye masu amfani ga al’umma. Ya bayyana cewa burinsa shi ne samar da ingantattun hanyoyin bunƙasa rayuwar jama’a, tare da tabbatar da kyakkyawan shugabanci na gaskiya da adalci.  

"Hadin gwiwa tsakaninmu da shugabannin jam’iyya a matakin mazabu yana da matukar muhimmanci domin ciyar da ƙaramar hukumar Katsina gaba. Wannan ganawa na da nufin sada zumunci, neman shawarwari, da kuma karfafa gwiwa domin cimma nasara a babban zaɓe mai zuwa," in ji Hon. Miqdad.  

Shugabannin mazabun da suka halarci taron sun nuna matuƙar jin daɗinsu, inda suka yabawa Hon. Miqdad bisa wannan tsari da ya fito da shi. Sun bayyana cewa za su bayar da cikakken goyon baya, tare da yin aiki tukuru domin ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben da ke tafe.  

Taron na ci gaba da gudana, kuma ana sa ran sauran mazabun za su samu damar jin shirye-shiryen da Hon. Miqdad ke da su domin al’ummar ƙaramar hukumar Katsina.

Follow Us