Bala Abu Musawa Ga Mustapha Inuwa: "Siyasa Ta Sake Ka, Ya Kamata Ka Koma Masallaci Ka Yi Istigfari"

top-news

Daga Muhammad Ali Hafizy, @Katsina Times    

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Bala Abu Musawa, ya mayar da martani ga tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Dr. Mustapha Inuwa, dangane da kalaman da ya yi kan taron mika tutoci ga ‘yan takarar kujerun ciyamomi da APC ta gudanar a garin Ingawa makon da ya gabata.  

A wata hira da ya yi da manema labarai a gidansa da ke rukunin gidajen Barhim a Katsina, da yammacin Laraba, 29 ga watan Janairu, 2025, Bala Abu Musawa ya ce Dr. Mustapha Inuwa na da dabi'ar ganin cewa idan ba shi ne ya yi abu ba, to wannan abin bai dace ba.  

"A wurin Mustapha, idan ba shi ne ya aiwatar da abu ba, to babu kyau. Ya dauka cewa shi kadai ne ke iya yin abu daidai," in ji Bala Abu Musawa.  

Ya ci gaba da cewa, "Mutumin da ko a zaben fidda gwani bai iya lashe wa kansa ba, kuma a babban zabe bai iya lashe rumfar mazabarsa ba, ballantana kananan hukumarsa, me zai ce kan siyasar APC? Ya koma PDP ne kawai don ya zama mai wuka da nama a jam’iyyar. Lokacin da ya bar APC, yana tunanin zai iya yaudarar Yakubu Lado don ya samu iko a PDP."

Bala Abu Musawa ya kuma bai wa Dr. Mustapha Inuwa shawara da ya hakura da siyasa, ya koma masallaci ya dinga istigfari.  

"Ya kamata Dr. Mustapha ya fahimci cewa komai na duniya yana da iyaka. Siyasa ta sake shi, lokaci ya yi da zai bar ta, ya koma masallaci ya yi ta istigfari. Mu kuma sai mu yi fatan Allah Ya sa mu cika da imani. Wannan irin siyasar farafagabta kuwa ta wuce yanzu," in ji shi.  

A karshe, ya bukaci mambobin APC a jihar Katsina da su fahimci cewa kalaman Dr. Mustapha Inuwa sun nuna yana cikin danasanin barin jam’iyyar.  

"Sakonmu ga ‘yan jam’iyyar APC shi ne, yanzu ne Dr. Mustapha ke fahimtar kuren sa. Yana jin haushin barinmu, kuma yana fahimtar cewa shayi ruwa ne. Idan ya ci gaba da wadannan maganganun, lokaci zai zo da za a sake gwada karfin siyasa. Amma ba za mu yarda da siyasar cin mutunci ba. Muna fatan Allah Ya shirye shi," Bala Abu Musawa ya kammala.

Follow Us