Shettima Ya Buɗe Taron Gwamnonin Yankin Tafkin Chadi, Ya Jaddada Bukatar Hadin Gwiwa Don Magance Matsalolin Tsaro

top-news



Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a yau wajen buɗe taron Gwamnonin Yankin Tafkin Chadi karo na biyar da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.  

Taron, wanda Gwamnatin Jihar Yobe ta dauki nauyi, ya hada gwamnonin jihohi takwas daga Najeriya, Kamaru, Chadi da Jamhuriyar Nijar, tare da kungiyoyin jin ƙai da ƙungiyoyin kasa da kasa, domin tattauna matsalolin tsaro da neman hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a yankin.  

A jawabin da ya gabatar a madadin Shugaban Kasa, Shettima ya bukaci a ɗauki matakai masu yawa don yaki da ta’addanci da sauran barazanar tsaro da suka addabi yankin Tafkin Chadi.  

Ya jaddada cewa rikice-rikicen da suka addabi yankin tsawon shekaru 15 da suka gabata na bukatar amfani da iko cikin hikima, domin tabbatar da tsaron rayuka da walwalar al’umma.

Follow Us