Hukumar AUDA-NEPAD ta shirya taron hadin kan 'yan jarida da hukumar, don sauya labarin Afirka

top-news

@Katsina Times 


Hukumar AUDA-NEPAD ta shirya taron tattaunawa da ‘yan jarida, inda ta bukaci hadin kai tsakanin manema labarai da kwararru a fannin yada labarai domin sake fasalta labarin Afrika da kuma tallata nasarorin hukumar bisa tsare-tsaren ci gaban da aka tsara a karkashin Ajandar Kungiyar Tarayyar Afrika ta 2063.  

Sabon Kwamishinan Kasa kuma Babban Darakta na AUDA-NEPAD, Alhaji Jabiru Salisu Abdullahi, ya jaddada muhimmancin rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen nuna nasarorin da aka cimma. Ya ce, “Kafafen yada labarai suna da karfin nuna nasarori, ci gaba, da tasirin shirye-shiryen AUDA-NEPAD. Ta wannan hanya, za mu iya canza labarin Afrika daga matsaloli zuwa labarin juriyarta, kirkira, da dama marasa iyaka.”  

Taron ya kare da sabon alkawari daga ‘yan jarida na yin aiki tare da AUDA-NEPAD wajen karfafa tafiyar ci gaban Afrika. An amince cewa hadin gwiwa tsakanin AUDA-NEPAD da kafafen yada labarai zai kara wayar da kan al’umma game da manufofin hukumar tare da kawo canji mai ma’ana a fadin kasar da nahiyar baki daya.