Gwamnatin Katsina Ta Sha Alwashin Kare Muradun Al’ummar Gozaki Kan Batun Sayar da Gonakai
- Katsina City News
- 20 Jan, 2025
- 17
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina ta tura tawaga ta musamman karkashin jagorancin Sakataren Gwamnati, Abdullahi Garba Faskari, domin sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar ƙauyen Gozaki dangane da zargin sayar da gonakinsu ga wani kamfani na ƙasar China. Wannan mataki ya biyo bayan koke-koken al’ummar yankin da ke nuna damuwa kan yuwuwar rasa wuraren gonakinsu waɗanda suka kasance tushen rayuwarsu da ci gabansu na tattalin arziki.
Bayan isar tawagar gwamnatin jihar a tsohon garin Gozaki, an tarar da taron al’umma, inda mazansu, mata, yara, da manya suka fito dauke da kwalaye masu kira da a tabbatar da adalci. Al’ummar yankin sun bayyana cewa ana ƙoƙarin kwace masu gonakai domin gina wurin shakatawa ga wani kamfani na ƙasar China, lamarin da suka ce zai jefa su cikin mawuyacin hali.
Da yake magana a wurin taron, Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙafur, Hon. Garba Abdullahi Kanya, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina ba za ta bari wani abu ya tauye haƙƙin al’ummar yankin ba. "Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, gwarzon al’umma ne. Ya jajirce wajen kare muradun jama’a, kuma ina da yakinin cewa wannan matsala za a warware ta cikin lumana," in ji shi.
Hakimin Gundumar Ƙafur, Alhaji Abdurrahman Abdullahi Rabe, ya goyi bayan wannan mataki na gwamnati, yana mai cewa, “Sarakuna suna tare da jama’a, kuma ba za mu lamunci duk wani abu da zai cutar da al’umma ba. Mun bayyana wa al’ummar Gozaki cewa duk wani yunkuri na yankar gonakai ya sabawa dokar da gwamnati ta shimfiɗa."
Shugaban Ƙungiyar Gozaki, Malam Yushai’u, ya bayyana muhimmancin gonakin ga rayuwar al’umma. "Gonakin nan ba kawai wurin noma ba ne, har ma tushen tallafa wa rayuwar yara da iyayensu. Wannan wuri shine makoma gare mu," in ji shi.
Wani mazaunin ƙauyen, Malam Abubakar Umar, ya gode wa Gwamna Dikko Radda bisa turo tawaga don sauraron matsalarsu. "Muna roƙon gwamnati da ta duba wannan batu da idon rahama saboda idan aka kwace mana gonaki, rayuwar mu za ta kasance cikin mawuyacin hali," ya bayyana.
A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, ya tabbatar wa al’ummar Gozaki cewa gwamnati za ta yi aiki tukuru don ganin an samar da mafita cikin lumana. “Mun ji duk ƙorafinku, kuma za mu isar da wannan batu ga mai girma Gwamna. Gwamnatin Katsina za ta tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙin ku,” in ji shi.
Lamarin kauyen Gozaki ya jaddada irin rawar da gonakin ke takawa a ci gaban tattalin arziki da tsaron rayuwar al’umma. Gonakai suna samar da abinci, kudin shiga, da ma’aikata ga al’umma, kuma rasa su na iya haifar da tashe-tashen hankula da rashin zaman lafiya. Gwamnatin Katsina ta nuna jajircewa wajen kare muradun jama’a, matakin da ke karfafa dangantaka tsakanin gwamnati da al’umma, tare da tabbatar da ci gaba mai dorewa.