Haɓɓaka Ilimi: Wata Gidauniya A Kaduna Ta Karrama Gwamnan Zamfara
- Katsina City News
- 20 Jan, 2025
- 38
Ranar Sabacin nan ne Gidauniyar Ci Gaban ilimi ta Masarautar Lere (Lere Educational Foundation) da ke jihar Kaduna ta karrama gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal da lambar yabo bisa irin gudumawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ci gaban ilimi a jihar Zamfara, da ƙasa baki ɗaya.
Da yake miƙa masa lambar yabon, Sarkin Lere injiniya Suleiman Umaru Lere, ya bayyana gamsuwarsa dangane da ƙoƙarin Gwamna Dauda Lawal wajen bunƙasa harkar ilimi, wanda hakan ya sanya gidauniyar ta bashi wannan lambar karramawa.
Taron wanda aka shirya shi domin bikin cika shekara Goma sha tara da kafa makarantar tunawa da Umaru Mohammed dake Lere, ya gudana ne a ɗakin taro na Otel ɗin Assa Pyramid da ke jihar Kaduna.
Sarkin na Lere ya ce, "Gwamna Dauda ya daɗe yana taimaka wa wannan gidauniya, ba tun yanzu ba. Saboda haka muna yaba masa matuƙa; muna kira ga sauran mutane sa suyi koyi da Dauda Lawal musamman a ƙoƙarinsa na bunoasa ilimi.
" Wannan gidauniyar tana matuƙar alfahari da gwamnan jihar Zamfara da abokansa, irin su Farfesa Kabiru Mato bisa yadda suke ba mu gudummawa wajen tallafa wa ci gaban ilimi a Lere, yau ga shi kowa ya ga abin da ya yi yau, wanda hakan yake tabbatar da cewa mutum ne jajirtacce
" Wannan makaranta da muke bikin cikarta shekara 19, an kafata ne domin tallafa wa yara marasa galihu wanda Alhamdulillah, bisa irin gudumawar da muke samu daga wurin ɗaiɗaikun mutane irinsu Dauda Lawal, shi ya kai ga har yanzu ana tafiyar da makarantar cikin nasara."
Gwamna Dauda Lawal, wanda ya samu wakilcin Babban Sakataransa na musamman ( PPS) Alhaji Munnir Baba, ya bayyana jin daɗinsa da wannan karramawar da aka yi mas, inda ya ce gwamnatinsa tana baiwa harkar ilimi Muhimmaci, wanda hakan ya sanya gwamnatin jihar Zamfara ta zama kan gaba a ɓangaren ilimi a Arewacin ƙasar nan.
A nasa jawabin, Shugaban kwamitin shirya taron, Malam Aliyu Lere ya bayyana cewa an shirya taron ne domin bikin cika shekara Goma sha tara da kafa makarantar, da kuma bayar da lambar yabo ga waɗanda suka bayar da gudumawa wajen ci gaban harkar ilimi a yankin Lere da sauran wurare.
Yana mai cew, an samar da makarantar ne domin tallafa wa yara marasa galih, wanda yanzu makarantar ta samar da Manyan Likitoci da Malaman Jami'o'i, wanda yanzu suke bayar da tasu gudummawar a ɓangarori daban-daban na rayuwar al'ummar.
A kan hakan, ya buƙaci masu hannu da shani da su tallafa wa gidauniyar domin ƙara inganta harkar ilimi a makaranta, musamman ganin cewa makarantar ta al'umma ce wacce take buƙutar tallafi ta ɓangarori da dama