"Ku Daina Wasan Siyasa da Addini" - Farfesa Sani Abubakar Lugga
- Katsina City News
- 19 Jan, 2025
- 148
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 19 Ga Janairu, 2025
Farfesa Sani Abubakar Lugga, Wazirin Katsina na Biyar, ya yi kira mai ratsa zuciya ga malamai da al’ummar Musulmi na Najeriya su daina amfani da addini wajen Yin siyasa. A wata hira ta musamman da Katsina Times a gidansa ranar Lahadi, ya yi gargadi kan barazanar da ke tattare da siyasantar da addini, yana danganta irin matsalolin da suka faru baya da makamancin haka a yanzu.
A cikin tattaunawarsa, Farfesa Lugga ya tunatar da zabukan 1993 da suka samu takarar "Muslim-muslim Ticket" wato Cif MKO Abiola da Baba Gana Kingibe. Ya bayyana yadda zabukan suka jefa ƙasar cikin rikice-rikice na siyasa wanda ya kai ga rasuwar shahararrun shugabanni, ciki har da Janar Shehu Musa Yar’Adua, Janar Sani Abacha, da Cif Abiola a cikin gajeren lokaci.
“Muna wasa da addinin Musulunci,” in ji Farfesa Lugga cikin gargadin. Ya kara da tunatar da yadda a shekarar 1997 aka gayyaci malamai zuwa Abuja domin karanta Al-Qur’ani mai girma sau miliyan ɗaya, amma matsalolin ba su kare ba. Ya bayyana damuwarsa cewa irin wannan yanayi na iya maimaita kansa, musamman ganin zabukan 2023 da suka sake samun takarar "Muslim-muslim Ticket", wanda ya kawo rashin tsaro, tsadar rayuwa, da matsalolin zamantakewa.
Haka kuma, Farfesa Lugga ya nuna damuwa kan shirye-shiryen da wasu malamai ke yi na tattaro mutane 60,000 don yin karatun Al-Qur’ani a Abuja, yana mai cewa abin da ya fi dacewa shi ne yin tuba tare da gyara halayenmu.
“Mu roƙi Allah ya shiryar da mu ta yadda za mu warware matsalolinmu maimakon ƙirƙirar sabbin matsaloli,” in ji shi, yana mai roƙon al’ummar Musulmi su koma ga Allah cikin gaskiya tare da fifita zaman lafiya da haɗin kai.
Wazirin ya kammala maganar sa da addu’a don samun tsari mai kyau daga Allah, yana mai kira ga al’umma da su guji kuskuren baya tare da rungumar sauyi mai ma’ana. A karshe ya mika sakon fatan alheri ga ƙasa da 'yan ƙasa.
Wannan hira ta musamman ta nuna muhimmancin warware matsalolin Najeriya cikin hikima da fifita haɗin kai, musamman duba ga darussan tarihi da ke koyar mana.