Kungiyar Dikko Project Ta Hada Gwiwa da Katsina Youth Craft Village Don Tallafawa Matasa
- Katsina City News
- 16 Jan, 2025
- 19
Kungiyar Dikko Project Ta Hada Gwiwa da Katsina Youth Craft Village Don Tallafawa Matasa
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Alhamis, 16 ga Janairu, 2025, Kungiyar Dikko Project a karkashin jagorancin Musa Yusuf Gafai ta kai ziyara ta musamman zuwa Katsina Youth Craft Village da ke Sansanin 'Yan Yi wa Kasa Hidima (NYSC) a kan Hanyar Mani, cikin birnin Katsina.
Da yake jawabi yayin ziyarar, shugaban kungiyar, Dokta Musa Gafai, ya bayyana dalilin ziyarar, inda ya ce, "Mun zo nan domin neman hadin kai da kuma yin aiki tare da wannan cibiyar horaswa. Muna yaba da irin kokarin da wannan makaranta ke yi wajen karfafa matasa da koya musu sana’o’in da za su dogara da kansu tare da basu jari. Cigaban da wannan cibiyar ta samu a karkashin jagorancin Dokta Dikko Umar Radda ya yi daidai da manufofinmu na tallata tsare-tsaren gwamnan jihar Katsina."
A nasa jawabin, babban ko’odinetan makarantar, Injiniya Kabir Abdullahi Kofar Soro, ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara, tare da jinjinawa hangen nesa da kwazon Dokta Musa Gafai. Ya kuma tabbatar da cewa makarantar za ta hada kai da kungiyar domin tallafawa matasa a jihar Katsina.
Injiniya Kabir ya bayyana Dokta Musa Gafai a matsayin ginshiki mai muhimmanci a karamar hukumar Katsina, wanda zai taka rawa wajen taimakawa gwamnatin Malam Dikko Umar Radda. Ya ce, "Na san Musa tun tuni, kuma na san irin kokarinsa da kishin jiharsa. Shi masoyi ne na gaske ga gwamna. Duk abin da ya kawo ga wannan cibiyar, za mu aiwatar da shi, domin mun san tunaninsa daya ne da na gwamna, ba zai taba kawo mana wani abu da zai kawo cikas ba."
Ziyarar ta samu rakiyar kansiloli daga mazabu daban-daban na karamar hukumar Katsina, da kuma wasu mambobin kungiyar Dikko Project. An yi maraba da wannan ziyara da karfin guiwa, wanda ya nuna cewa kungiyar ta shirya tsaf domin gudanar da manyan ayyuka na tallafawa manufofin gwamnatin Dikko Umar Radda a jihar Katsina.
Kungiyar Dikko Project na kara nuna jajircewa wajen bunkasa matasa da karfafa tattalin arziki a jihar Katsina ta hanyar irin wannan hadin gwiwa.