An Yi Taron Cikar Jaridar Amizan Shekaru 35 A Kano.

top-news

Auwal Isah, Zaharaddeen Ishaq Abubakar 

Dadaddiya kuma shahararriyar jaridar nan da ake wallafawa da harshen Hausa a garin Zariya jihar Kaduna, ALMIZAN, ta shirya taron bikin cikarta shekaru 35.

Bikin wanda ya gudana jihar Kano, an shafe tsawon Yini Uku ne ana gudanar da shi a ranakun Juma'a zuwa Lahadi, 10 zuwa12 ga Rajab, 1445 Hijira (10 zuwa 12 ga Jainarun, 2025 Miladiyya)

A ranar farko ta taron, an gudanar gudanar da tattaunawar sada zumunci ne tsakanin wakilai da dillan jaridar wadanda suka fito daga garuruwa daban-daban.

A rana ta biyu kuwa, an gudanar da Lakcoci ne a kan mau'du'ai mabambanta irinsu: "Tsaftace Aikin Jarida A Wannan Zamani", "Fasahar AI: Amfani Da Matsalolinta", da kuma "Tasiri Da Muhimmancin 'Yanjarida A Rayuwar Al'umma" Lakcocin da Malam Al'ameen Chiroma Abuja, Injiniya Abbas Abdullahi Kaduna da Farfesa Isah Hassan Mshelgaru suka gabatar.

A rana ta uku kuma ta rufe taron da Maudu'an "Almizan A Shekaru 35: Inda Aka Taso, Inda Ake Da Inda Aka Dosa", "Fuskokin Aikin Jarida A Wannan Zamanin", da "Tsokaci A Kan Jaridar Al-mizan" su ne aka gabatar, maudu'an da suka suka samu gabatarwar kwarrun masana.

Hakazalika, jaridar da kuma karrama wasu mutane da ta kira "Gwarazan Al-mizan Guda 5" da suka hada da: Malam Ibrahim Musa, Farfesa Adamu Gwarzo, Marigayi Dakta Yusuf Ali, Kamfanin Media Trust, da Mawaki Sa'idu Sakafa Potiskum.

Kamar yadda Jaridun KatsinaTimes da Taskar Labarai suka tattaro, wadanda suka halarci taron kuma suka yi tsokaci a wajen sun hada da: Shugaban rukunin jami'o'in Maryam Abacha American Univedsity (MAAUN) Farfesa Mohammad Israr, Shugaban jami'ar Franco British University da ke jihar Kaduna  Farfesa Muhammad Sabo, Wakilin 'yan'uwa Musulmi na Kano Dakta Sanusi Abdulkadir, wanda ya samu wakilcin Farfesa Dauda Nalado daga jami'ar BUK, Shugaban Jami'ar MAAUN ta Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, Shaikh Misbahu Yusuf Ali, da  Malama Bilkisu Yusof Ali.

Sauran sun hada da: tsohon daraktan gudanarwa na jaridar Daily trust Naziru Mika'ilu Abubakar, Shugaban rukunin Jaridun KatsinaTimes, TheLinks da Taskar Labarai Alhaji Danjuma Katsina, Wakilin lauyoyin harkar Musulunci Barista Haruna Magashi, shugaban Kungiyar kare hakkin Bil'adama a Kaduna Kwamared Shehu Sani wanda ya samu wakilcin Kwamred Musa Baban Iya, Dantakarar shugaban karamar hukumar Dandume a karkashin jam'iyyar PDP Honorabul Abdullahi Usman Tumburkai, mataimakiyar shugaban jaridar Albishir Husaina Bichi da sauransu.

A tsawon shekaru 35 da jaridar Al-mizan din ta ratso, ta fuskanci barazana da kalubale kala-kala musamman daga hukumomi inda aka sha kama ma'aikata da dillanta tare da tsare su, wanda ko a baya-bayan nan a watan Satumban shekarar 2023, sai da jami'an tsaron farin kaya na DSS suka kama babban Editan jaridar, Ibrahim Musa, a filin sauka da tsashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, a lokacin da zai tafi kasa mai tsarki don yin Umrah.