MAJALISAR KOLI TA SHARI’A A NAJERIYA RESHEN JIHAR KATSINA TA GABATAR DA MATSAYAR TA AKAN KUDURIN SABUNTA HARAJI

top-news

Majalisar Koli ta Shari’a reshen Jihar Katsina ta jaddada matsayar al’ummar jihar kan kudirin sabunta haraji, tare da yin kira ga wakilan jihar a Majalisar Dokoki ta Tarayya da su dakile kudirin domin kare walwalar al’umma.

A ranar Juma’a, 10 Rajab 1446 (11 Janairu, 2025), Majalisar Koli ta Shari’a (Supreme Council for Shari’a in Nigeria, Katsina State Chapter) ta gabatar da takardar matsayarta kan batun sabunta haraji ga ‘yan Majalisar Dattawa da na Wakilai na Jihar Katsina a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da masana tattalin arziki da masu ruwa da tsaki suka gudanar.

Shugaban majalisar, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina, ya mika takardun matsayar ga wakilin ‘yan majalisun Katsina, Hon. Abubakar Yahaya Kusada, wanda ya samu wakilcin Hon. Sani Aliyu Danlami, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Katsina. Takardar ta yi kira ga ‘yan majalisun su tsayawa tsayin daka wajen dakile dokar harajin, tare da tunatar da su muhimmancin kare rayuwar al’ummar jihar daga tsadar rayuwa.

A cikin jawabinsa, Sheikh Yakubu Musa ya yaba wa ‘yan majalisar Katsina bisa kokarinsu na ganin dokar bata samu karbuwa ba. Ya kuma yi kira ga Allah ya taimaka wa wadanda ke kokarin dakile dokar da za ta jefa al’umma cikin wahala, tare da addu’ar Allah ya hana nasara ga masu goyon bayan dokar.

Dan Majalisar Wakilai, Hon. Sani Aliyu Danlami, ya jaddada cewa dukkan ‘yan majalisar Katsina suna da matsaya guda kan kudirin harajin. Ya bayyana cewa tun lokacin da aka gabatar da kudirin, suna gudanar da ayyuka tare don tabbatar da ba a aiwatar da dokar da za ta cutar da al’ummar jihar da ma kasa baki daya ba.

Takardar Matsayar Majalisar Koli ta Shari’a
A cikin takardar, Majalisar ta bayyana cewa kudirin sabunta haraji bai yi daidai da ka’idojin bunkasar tattalin arziki ba. Haka kuma, akwai wasu sashe na dokar da suka saba wa dabi’u da ka’idojin Musulunci.

Takardar ta kara da cewa:
"Mun yi la’akari da cewa duk wata doka ko tsari da zai shafi rayuwa da walwalar al’ummarmu dole ne a tsara su a hankali don tabbatar da gaskiya da daidaito. A saboda haka, muna kira ga wakilan Jihar Katsina da kada su goyi bayan wannan kudiri."

Taron ya samu halartar malamai da wakilan kungiyoyin fararen hula, ciki har da shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula na Jihar Katsina, Comr. Abdurrahman Abdullahi.

Majalisar Koli ta Shari’a ta bayyana cewa za ta ci gaba da yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da kare hakkin al’umma daga duk wata doka da za ta jefa su cikin matsin rayuwa.