TATSUNIYA: Labarin Muwa Muwa
- Katsina City News
- 11 Jan, 2025
- 101
A wani daji mai nisa, an yi wata rakumar dawa mai suna Muwa. Ta kasance rakumiya guda tilo, ba ta da dangi ko 'yan uwa. Kowacce rana da ta dawo daga kiwo, sai ta kasance cikin baƙin ciki tana kuka saboda rashin haihuwa. Sai dai, cikin ikon Allah, wata rana ta haifi 'ya'ya hudu.
Saboda farin ciki da wannan gagarumar nasara, sai ta rada wa babbar cikinsu suna Muwa Muwa, ta rada wa ta biyun suna Caccikarimba, sai na ukun kuma Malaladumba. Amma na hudun, wanda ya fito a rame, ba ta ba shi suna. Saboda yadda ba ta son shi, ta yi watsi da shi, ta ƙi kulawa da shi.
Rakumar ta yi ƙauna sosai ga 'ya'yanta uku na farko. Don haka, ta gina musu ɗaki mai ƙarfi, ta tsare su daga ruwa da kura. Sai dai ta bar ƙaramin a waje, tare da cewa, idan ya rayu to ya rayu, idan kuma ya mutu, babu ruwanta. Ta kuma umurce su da cewa:
"Idan kun ji muryata, ku buɗe kofa. Amma idan ba muryata ba ce, kada ku buɗe!"
Muryar Kura
Kullum idan rakumar ta dawo daga kiwo, sai ta kira su da muryar ta mai daɗi tana cewa:
"Muwa, Muwa zo ka sha,
Caccikarimba zo ka sha,
Malaladumba zo ka sha."
Suna jin haka, sai su fito su sha nono, su koma ciki. Wata rana, wata Kura tana wucewa, sai ta ji rakumar tana kiran 'ya'yanta. Kura ta yi sha'awar cinye yaran, amma muryarta ba ta yi kama da ta rakumar ba. Sai ta yi ƙoƙari ta yi kiran kamar haka:
"Muwa, Muwa zo ka sha,
Caccikarimba zo ka sha,
Malaladumba zo ka sha."
Amma yara suka gane ba muryar mahaifiyarsu ba ce, suka yi ihu suka ƙi buɗe kofa. Wannan abu ya ɓata wa Kura rai, amma ta tafi don neman mafita.
Muryar Karya
A kan hanya, Kura ta hadu da wani Biri mai ba da magani. Sai ta roƙe shi ya ba ta maganin da zai mayar da muryarta kamar ta rakumar dawa. Biri ya ce zai iya yi mata hakan, amma da sharadin ba za ta ci komai ba har sai ta gama amfani da maganin. Kura ta amince, ta karɓi maganin, kuma nan take muryarta ta zama kamar ta Muwa.
Da wannan sabon salo, sai Kura ta koma bakin kofar yaran rakumar. Ta kira su da muryar da ta yi kama da ta mahaifiyarsu:
"Muwa, Muwa zo ka sha,
Caccikarimba zo ka sha,
Malaladumba zo ka sha."
Yaran, ba tare da wata shakka ba, suka buɗe kofa. Sai Kura ta yi wuf ta cinye su gaba ɗaya, sannan ta bar wurin.
Dawowar Mahaifiya
Da Muwa ta dawo gida, kamar yadda ta saba, ta kira 'ya'yanta:
"Muwa, Muwa zo ka sha,
Caccikarimba zo ka sha,
Malaladumba zo ka sha."
Sai ƙaramin ɗan da ta bari a waje ya ce:
"Muwa, Muwa ba ya nan,
Caccikarimba ba ya nan,
Malaladumba ba ya nan."
Muwa ta ji tsananin baƙin ciki. Sai ta ce masa:
"To, kai ma zo ka sha."
Daga wannan rana, Muwa ta fara ƙaunar ƙaramin ɗan nata, har ma suka zama abokan tafiya. Duk inda za ta tafi kiwo, sai su tafi tare.
Darussan Labarin
1. Bai kamata iyaye su nuna bambanci tsakanin 'ya'yansu ba, domin kowanne na da nata fa'idar.
2. Wahala ba ta dawwama; akwai mafita daga kowacce matsala.
3. Mai rabon gani, dole zai rayu ko da halin ƙunci ya yi yawa.
4. Kyautatawa ga wanda aka raina na iya haifar da ƙauna a ƙarshe.