GWAMNA LAWAL YA GANA DA MINISTAN BUNƘASA KIWON DABBOBI, YA CE ZAMFARA TA SHIRYA WA KIWO
- Katsina City News
- 10 Jan, 2025
- 99
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwon Dabbobi cewa jihar Zamfara na da wuraren da za a yi kiwo.
A ranar Alhamis ne gwamnan ya ziyarci hedikwatar ma’aikatar a wata ziyarar ban girma da ya kai wa ministan, Alhaji Idi Mukhtar Maiha.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa, jihar Zamfara, kasancewarta jihar noma da kiwo tana taka rawar gani a aikin ma'aikatar binƙasa kiwon dabbobi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an ƙirƙiro ma’aikatar ne a watan Yulin 2024 domin gyara masana’antar kiwon dabbobin Nijeriya, da samar da yanayi mai inganci, da ƙarfafa zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje, da kuma inganta samar da abinci.
A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya bayyana aniyar gwamnatinsa na haɗa kai wajen lalubo baiwar da jihar Zamfara ke da shi.
“Minista, kamar yadda ka sani, Zamfara al’umma ce ta noma. Shi ya sa taken mu shi ne, ‘Noma Abin Alfaharinmu Ne’.
“Mun zo nan ne a yau domin taya ku murna da kafa wannan sabuwar ma’aikatar, wadda nake da yaƙinin ta dace. Bugu da ƙari, muna da burin samar da haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin jihar mu da ma'aikatar.
“A Zamfara, madatsun ruwa da dama a faɗin jihar na buƙatar gyara don samar wa dabbobi da ruwa, haka kuma za a iya samun damar ɗaukar duk wani shiri.
"Muna gayyatar Minista da tawagarsa da su ziyarci Zamfara domin duba yanayin kiwo na jihar."
A lokacin da yake mayar da martani, ministan harkokin kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ya gode wa gwamna Lawal bisa ziyarar da ya kai ma'aikatar.
“Tun da aka kafa ma’aikatar, ba mu samu ziyarar wani gwamna mai zartarwa da ke da buƙatar jin abin da za mu iya bayarwa ba.
“Ina so in tabbatar muku cewa a shirye muke mu ba ku haɗin kai don kawo sauyi da magance matsalolin ku a fannin kiwon dabbobi a Zamfara.
“Bangaren kiwo ya daɗe yana aiki ba bisa ƙa’ida ba. Za mu zamanantar da wannan fanni ta hanyar tsare-tsare daban-daban.
“Gwamna, jihar Zamfara ce za ta zama jihar da za ta yi gwaji domin nuna ajandar sabuwar ma’aikatar. Da wannan haɗin gwiwa za mu mayar da Gidan Jaji da ke Zamfara wata ƙaramar cibiyar kiwo,” inji ministan.