Gwamnatin Tarayya Za Ta Karɓi Ragamar Makarantun Tsangaya 157 da Aka kafa
- Katsina City News
- 10 Jan, 2025
- 74
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na karɓar mallakar makarantu 157 na almajirai da aka kafa a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, waɗanda aka mika wa gwamnoni na jihohin Arewa 19.
Sakataren Zartarwa na Hukumar Almajirai da Yara Masu Barin Makaranta (NCAOSC), ya bayyana haka yayin wani taron rattaba hannu kan yarjejeniya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Civil Society Action Coalition on Education for All (CSACEFA) a Yola, Jihar Adamawa.
A cewarsa, gwamnatin da ta gabata tayi watsi da wadannan makarantu:
"Na umarci Shugaban Ma’aikatana da ya kammala shirye-shiryen karɓar makarantun almajirai 157 da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya gina, waɗanda gwamnatin da ta gabata suka yi watsi da su.
"Haka nan, mun nemi Gwamnatin Tarayya da ta taimaka mana wajen gyara wadannan makarantu don fara gudanar da ayyukan karatu cikin tsari a kokarinmu na magance matsalolin almajirai da yara da basa zuwa makaranta a ƙasar nan," in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa hukumar tana aiki tare da Hukumar Nazarin Larabci da Karatun Addinin Musulunci ta Ƙasa (NBAIS) don tura ma'aikata zuwa makarantun da aka gyara, la'akari da yawansu.