TAWAGAR GWAMNATIN KATSINA TA ISA KASAR MASAR DON DUBA DALIBAI MASU KARATUN AIKIN LIKITA.
- Katsina City News
- 08 Jan, 2025
- 94
@ Katsina times
Babbar tawagar gwamnatin jahar Katsina, karkashin jagorancin Mai girma Mataimakin gwamnan Katsina, Malam faruk lawal Jobe, sun kai ziyara kasar Masar, domin ganawa da jami an Makarantar da Daliban jahar Katsina ke karatun aikin likita.
Tawagar za ta kuma yi Nazari da bitar yadda karatun daliban ke tafiya, za su kuma gana da daliban don jin ta bakin su, yadda karatun ke gudana.
Tawagar zata kammala biyan kudin karatun daliban na shekaru biyar cif, ciki harda kudin alawus din daliban na wata wata.
Tawagar zata yi kokarin samarwa jahar Katsina gurbin karatu wanda hukumar Makarantar kan dau nauyi dari bisa dari.
Ga hotunan ziyarar da tawagar ta kai jami ar Nahda dake kasar ta masar inda daliban ke karatu.