Harin Borno: Mun kashe ƴan ta’adda 34 amma mun rasa jami'ai 6 – Sojoji
- Katsina City News
- 08 Jan, 2025
- 90
Shelkwatar tsaro ta kasa, a yau Laraba, ta bayyana yadda rikici ya faru tsakanin ƴan ta’adda da jami’an bataliyar 'Forward Operating Base' a yankin Sabon Gari, karamar hukumar Damboa, jihar Borno.
Rundunar sojin ta tabbatar da cewa sojoji 6 sun rasa rayukansu yayin fafatawar, yayin da aka kashe ƴan ta’adda 34 da su ka yi kokarin kai wa sojojin hari don daukar fansar kashe kwamandansu da wasu mayakansu kwanan nan.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa kwana hudu bayan ƴan ta’addan Boko Haram sun kwace sansanin sojoji, har yanzu ba a ga wasu sojojin ba – al’amari da wasu manyan jami’an tsaro su ka bayyana da cewa “mai tayar da hankali.”
Da safiyar yau Laraba, Daraktan yada Labarai na Tsaro, Edward Buba, ya bayyana cewa mafi yawan gawarwakin da aka gano na ‘yan ta’adda ne.
Buba, ya sanar da cewa ƴan ta’addan sun hallaka ne ta hanyar harin sama da rundunar 'Operation HADIN KAI l' ta kai.
A cewarsa, rahoton kimanta barnar ya nuna cewa an kashe ƴan ta’adda da dama, sannan an ƙwato makamai daga hannunsu.
Daily Nigeria Hausa