'Yan Bindiga Sun Kona Gidaje da Coci a Ƙaramar Hukumar Kajuru, Kaduna
- Katsina City News
- 03 Jan, 2025
- 146
Wasu 'yan bindiga sun kai hari a unguwar Rogo, da ke cikin al'ummar Ugom a gundumar Maro, Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, a ranar Sabuwar Shekara, inda suka yi barna mai yawa.
Zamani Ishaku, wani mazaunin Maro, ya tabbatar wa wakilinmu da harin, yana bayyana cewa yankin ya dade yana fama da hare-haren 'yan bindiga ba kakkautawa.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar Ci Gaban Ugom, Onussim Ishaya, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa maharan sun lalata Cocin ECWA da ke Unguwar Rogo tare da ƙone ta bayan sun yi sata a coci da gidan faston cocin.
"Al’ummar garin duk sun tsere zuwa daji, suna barin dukiyoyinsu don tsira da rayukansu," in ji Onussim.
Ya yi kira ga gwamnatocin matakai daban-daban su gaggauta ɗaukar mataki kan lamarin, yana mai cewa abin ya ɗaure zuciya ganin irin wannan tashin hankali a farkon shekara.
Haka kuma, ya nemi addu’o’i daga al’umma da kuma ƙara girke jami’an tsaro a yankin.
Ƙoƙarin jin ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ci tura, domin ba a samu amsar kira da sakonnin da aka aika masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.