Rundunar ‘Yan Sanda Ta Katsina Ta Bayyana Nasarorin Da Ta Cimma a Shekarar 2024
- Katsina City News
- 03 Jan, 2025
- 92
2 Ga Janairu, 2025 | Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Katsina Times
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da manyan nasarorin da ta samu wajen yakar laifuka da tabbatar da tsaro a fadin jihar a shekarar da ta gabata. Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Alhamis a hedkwatar rundunar, Kakakin Rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya gabatar da bayanai a madadin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Aliyu Abubakar Musa.
ASP Aliyu ya fara jawabin ne da nuna godiya ga Gwamnatin Jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, tare da godiya ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, bisa goyon bayan da suke bai wa rundunar a fannoni daban-daban. Ya kuma yaba wa jami’an rundunar bisa jajircewarsu wajen ganin an tabbatar da tsaro a jihar.
A cikin bayanansa, ASP Aliyu ya lissafo manyan nasarorin da rundunar ta cimma a shekarar 2024 kamar haka:
An ceto mutane 319 daga hannun masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga tare da hadasu da iyalansu.
An kashe ‘yan bindiga 40, wanda ya rage musu karfin aikata laifuka.
An kama barayin shanu 81 tare da dawo da shanu 2,081 ga masu su.
An kama ‘yan fashi 199, wanda ya kara tsaro a kan titunan jihar.
An kama fiye da mutum 100 da ake zargin masu fyade ne da kuma masu aikata luwadi.
An gurfanar da manyan dillalan miyagun kwayoyi 23 a kotu.
An gurfanar da masu lalata kadarorin jama’a 32 a kotu.
An kama masu satar motoci 89 tare da dawo da motoci da babura 27 da aka sata.
Rundunar ta nuna wasu kayayyaki da ta gano daga hannun masu laifi, wanda suka hada da:
1. Bindigogi kirar AK-47 guda hudu da bindigogi na gargajiya guda 13
2. Bindiga kirar pump-action guda daya da makamai na AK-47 guda 17
3. Alburusai guda 740 masu rai
4. Kayan sarki na ‘yan sanda da sojoji
5. Motoci da babura guda 10 da ake zargin an sata
6. Wutar lantarki da aka lalata da kuma miyagun kwayoyi
A karshe, ASP Aliyu ya gode wa manema labarai bisa hadin kan da suke bai wa rundunar wajen yada labarai cikin gaskiya da adalci. Ya kuma gode wa al’ummar jihar Katsina bisa goyon baya da hadin kan da suke bai wa jami’an tsaro.
Ya bukaci al’umma su ci gaba da ba da goyon baya ga hukumomin tsaro domin ci gaba da samun zaman lafiya mai dorewa a jihar.
Rundunar ta tabbatar da kudirinta na ci gaba da yaki da dukkan nau’o’in laifuka da kare rayukan al’ummar jihar Katsina.