Kungiyar Marubuta Labaran Wasanni Ta Rantsar Da Sabbin Shugabanninta Na Jihar Katsina.
- Katsina City News
- 01 Jan, 2024
- 120
Auwal Isah Musa, Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Kungiyar marubuta labaran wasanni ta kasa reshen jihar Katsina, SWAN, ta rantsar da sabbin shugabanninta a matakin jiha.
An dai gudanar da taron rantsawar ne a ranar 1 ga watan Janairun nan na 2025 a Sakateriyar kungiyar 'yanjarida ta jihar Katsina, rantsarwar da Barista Umar Kabir Darma ya jagoranta.
Da yake jawabi jim kadan bayan rantsarwar, Shugaban 'Yanjarida na kasa reshen jihar Katsina (NUJ), Kwamared Tukur Dan Ali, ya hore sabbin shugabbanin kungiyar ta SWAN da suka zage damtse su yi abin da ya kamata a cikin damar da suke da ita ta wa'adin shugabancinsu na shekaru uku, domin su zama abin koyi ga na bayansu.
Kwamared Dan Ali, ya bayyana tsohon shugaban kungiyar ta jiha, Abdullahi Muhammad Tanko, a matsayin magabaci abin koyi a kungiyar, domin ya rike kungiyar tsawon shekaru uku ba tare da an same shi da wata matsala ba.
Dan Ali, ya kuma bada tabbacin ba wa kungiyar ta SWAN cikakken goyon baya, don kai jihar Katsina kololuwar nasara a bangaren labaran wasanni ba kawai a jiha ko a Arewacin Nijeriya ba, a'a har ma da kasa baki daya.
Rantsarwar ta samu halartar manyan mutane da suka hada da: Shugaban kungiyar marubuta labaran wasannin na kasa, Isaiah Benjamin, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar gudanarwa ta wasanni ta kasa Malam Ibrahim Malikawa, Sakataren kungiyar kwallon kafa ta Katsina United Malam Mas'udu, Wakilin daraktan hukumar wasanni ta jiha Malam Yusuf Lawal, da shugaban kamfanin AA Rahamawa Aminu Ahmed Wali, da sauransu.