ZUWAN HILLSIDE ALHERI NE A JAHAR KATSINA
- Katsina City News
- 01 Jan, 2025
- 174
...Nazarin jaridun Katsina Times
Wani katafaren masaukin baƙi mai suna HILLSIDE da aka gina a unguwar Gidan Dawa da ke birnin Katsina, ya zama alheri ga marayu, mabuƙata da marasa ƙarfi a jihar Katsina.
HILLSIDE, wuri ne da aka gina wanda yake masaukin baƙi na alfarma da kuma ɗakunan taro, wanda yake da matsayi daidai da na ko'ina a duniya.
Wani mai kishin bunƙasa da cigaban jihar Katsina da Arewa maso Yamma, ya kawo shi Birnin Dikko domin samar da masauƙi na alfarma don buƙatar matafiya, maziyarta da masu neman wajen taro na zamani.
HILLSIDE, ya zo da tsarin masaukin baƙi mai tsari da ƙyautatawa na daidai da manyan otel-otal da ke faɗin duniya.
Matafiya da suka sauka a ciki sun misalta shi da wasu manyan masaukin baƙi guda uku da ake da su a Abuja da wasu huɗu a Legas da wasu a ƙasar Dubai.
Wani sabon salo da HILLSIDE ya zo da shi a shekarar farko da kafuwar sa shi ne, kafa Gidauniya wadda ya sanya wa suna HILLSIDE CHARITABLE FOUNDATION.
An tsara duk ribar da masaukin baƙin ya samar za a saka ta a wannan Gidauniyar.
An yi wa wannan Gidauniyar cikakkiyar rijista kamar yadda dokar ƙasa ta tsara, aka yi mata Kwamitin Amintattau da Shugabansu; Malam Maiwada Ɗanmalam. Aka yi mata Hukumar Gudanarwa, wacce Alhaji Ibrahim Jiƙamshi ke jagoranta. Aka yi mata ofis da tsarin aiki mai zaman kansa.
Gidauniyar ta tsara aiki gadan-gadan da ƙungiyoyi da wasu gidauniyoyi masu taimakon al'umma a ciki da wajen Nijeriya da kuma wasu Attajirai da suka daɗe suna wannan aikin.
A ranar Lahadi 29/12/2024, Gidauniyar HILLSIDE ta shirya gagarumin taro a ɗakin taronsu na Katsina, wanda suka tara manyan malamai na jihar Katsina, da fitattun mutane daga jihar, ƙungiyoyi masu zaman kansu da jami'an gwamnati, inda suka bayyana masu tarihin kafuwar HILLSIDE CHARITABLE FOUNDATION da ayyukan da ta yi daga kafuwar ta zuwa ranar taron.
A taron, shugaban sashen masaukin baƙin na HILLSIDE ROYAL SUITES, Alhaji Muttaƙa Jiƙamshi, ya bayyana cewa sun tsara duk ribar da suka samu wani kasafi ya tafi ga Gidauniyar.
Ya ce suna kuma haɗaka da duk wani mai son aikin cigaba.
Shugaban Kwamitin Amintattu na Gudauniyar, Malam Maiwada Ɗanmalam, godiya ya yi ga duk waɗanda suka ƙarfafa masu gwiwa da taimakon Gidauniyar.
Shi kuma shugaban Kwamitin Gudanarwar, Alhaji Safiyanu Jiƙamshi shi ne ya yi bayanin ayyukan da suka yi yayin da ɗakin taro ya yi tsit.
Wasu bayanan na tashin hankali ne. Misali wata mata da ke yawo da hanjin ta a waje, kuma ba ta da cin yau, balle na gobe.
HILLSIDE sun ɗau nauyin.ta, yanzu haka tana ƙasar Masar ana yi mata magani.
Wani bawan Allah ƙashin bayansa ya motsa, HILLSIDE suna tsaka da yi masa magani Allah ya ɗau ransa bayan sun kashe sama da Naira milyan uku.
An nuna Hotuna, tare da ba da labarai masu ratsa zuciya.
Shugaban ya kawo ayyukan da suka yi na gina rijiyoyin burtsatsai da kuma tallafi ga ilmi da karatu da wasu ayyukan alherin da suka yi da wasu gidauniyoyin.
HILLSIDE sun kammala tsari da shirin fara gina wani katafaren asibiti mai zaman kansa da babu kamar sa a ƙasar nan, wanda maimakon zuwa ƙasashen waje sai dai a zo Katsina.
A ranar taron Gidauniyar ta zaɓo wasu fitattun mutane a birnin Katsina da suka daɗe suna irin waɗannan ayyukan na taimakon al'umma suka karrrama su da nufin ƙarfafa masu gwiwar cewa, "An san abin da kuke, kuma Allah ne zai saka maku."
Ga jadawalin waɗanda aka karrama:-
TAIMAKO A AYYUKAN JINƘAI.
1.GIDAUNIYAR JAHAR KATSINA
2.LATE MALAM MUSA MATAWALLE 'YAR'ADUA.
3.LATE ALHAJI MANZO ABUBAKAR.
4.LATE SA'IDU UMAR
5.ALHAJI BILYA SANDA
6.ALHAJI AHMAD MUSA FILIN SAMJI
7.ALHAJI MUHAMMADU USMAN SARKI
8.ALHAJI ABU MODIBBO
taimakon marayu da gajiyayyu
1.Daawah Family Support
2.Malam Ashafa Abubakar
Taimakon harkar ilmi
1.Malam Adam Hussaini
2.Ideas and Data
3.Malama Murjanatu Ibrahim Duwan
4.Fityah Centre for da Awa Education
Kula da muhalli Marigayi Alhaji Aminu Mammam Dee
2.Katsina Youths Against Deforestation
Harkar isar da saƙo
Malam Ɗanjuma Katsina
Katsina Post
Ɓangaren tsaro
Late Ahmad Bashar Daura.