Bidiyo na Bogi: Kotu Ta Tura Mahdi Gidan Yari
- Katsina City News
- 01 Jan, 2025
- 93
Wata babbar kotun majistare da ke zama a Kaduna a ranar Talata ta ba da umarnin tsare Mahdi Shehu, wanda ya ke da’awar kasancewa mai fafutuka da sharhi kan al’umma, a gidan gyaran hali na Kaduna.
An kama Mahdi kwanaki kadan da suka gabata ta hannun jami’an Hukumar Tsaro ta DSS, bayan ya ki janye wasu bidiyoyi da ya wallafa a intanet, inda ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Faransa izinin kafa sansanin soji a arewacin Najeriya.
Zargin Mahdi ya biyo bayan wani irin ikirari da shugaban mulkin soja na Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani, ya yi cewa Faransa ta kafa sansanin soji a arewacin Najeriya. A cikin wani sako da ya wallafa, Mahdi ya dora alhakin yarjejeniyar kan Shugaba Bola Tinubu. Sai dai, Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Kasa (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, tare da Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, sun karyata wannan ikirari daga shugaban mulkin soja na Nijar a matsayin ba gaskiya ba.
A ranar Talata, DSS ta gurfanar da Mahdi a gaban Mai Shari’a Abubakar Lamido, bisa tuhumar aikata laifuka biyu: haɗa kai, tallafa wa ta’addanci, da tayar da tarzoma a bainar jama’a. Hukumar ta ce wannan ya sabawa Sashe na 26 (2)(3) na Dokar Hana Ta’addanci ta 2022 da kuma Sashe na 78 na Dokar Kundin Hukunta Manyan Laifuka ta Jihar Kaduna ta 2017.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Lamido ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Mahdi a gidan gyaran hali na Kaduna har zuwa ranar 14 ga Janairu, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
An tabbatar da cewa bidiyoyin da Mahdi ya wallafa ba na gaskiya bane, kamar yadda wasu kafafen watsa labarai, ciki har da Daily Trust da The Cable, suka bincika. Bidiyoyin dai na shekarar 2013 ne, suna nuna sojojin Najeriya a filin jirgin sama na Bamako, Mali, lokacin da ake tura su aikin kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka a arewacin Mali.