Taron Manema Labarai na Watan Disamba: Mataimakin Gwamnan Katsina Ya Gabatar da Jawabi Akan Kiwon Lafiya
- Katsina City News
- 31 Dec, 2024
- 160
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Talata, 31 ga watan Disamba, 2024, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruq Lawal Jobe, ya jagoranci taron manema labarai na karshen wata da aka gudanar a tsohon gidan gwamnatin jihar Katsina. Taron ya mayar da hankali kan manyan nasarorin da gwamnatin jihar ta cimma, musamman a fannin lafiya, tare da bayyana kudurorin da ke gaban ta domin inganta rayuwar al’umma.
Faruq Lawal Jobe ya bayyana cewa, Gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagoranci Malam Dikko Umar Radda PhD, ta kammala gina cibiyar wankin ƙoda da kuma samar da kayan aiki a Asibitin Kwararru na Janar Amadi Rimi da ke Katsina. Wannan asibiti, wanda aka bayyana yana cikin mafi inganci a Najeriya, an kashe N681,104,727.92 wajen aiwatar da aikin.
Haka kuma, an bayar da kwangilar gina cibiyar zamani ta bincike da daukar hoto a wannan asibiti, wanda aikin ya kai kimanin N13,137,170,677.93.
Domin magance matsalar sayar da magunguna marasa inganci, gwamnatin ta siyo magunguna masu nagarta daga kamfanoni, inda aka kashe N3,331,031,121. Bugu da ƙari, an gyara rumbun ajiyar magunguna tare da haɗin gwiwar “Global Fund” a kan N766,815,832.
Ya ce, Gwamnatin ta ci gaba da bayar da tallafi ga mata masu juna biyu, haihuwa ta hanyar tiyata, da wasu ayyuka na lafiya, inda aka kashe N397,000,000 a shekarar da ta gabata.
Malam Faruq Lawal ya bayyana yadda gwamnatin ta fara amfani da tsarin e-Health a asibitocin jihar, wanda kudinsa ya kai N244,440,000.
A Cikin jawabin nasa mataimakin Gwamnan ya bayyana yadda gwamnatin ta karfafa aikin hukumar KATCHMA, inda aka yi nasarar rajistar kaso 96% na ma’aikatan gwamnati cikin tsarin inshorar lafiya, tare da ƙarin mutane sama da 127,000 daga bangaren masu zaman kansu.
Malam Faruq Lawal ya bayyana wata Nasara da Gwamnatin jihar Katsina ta samu na Lambar yabo daga Nigerian Healthcare Excellence Award har sau biyu a jere, a matsayin jihar da ta yi fice wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya.
A karshe, Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina za ta ci gaba da aiki tukuru domin ganin an samu cigaba mai dorewa a rayuwar al’ummar jihar, musamman a bangaren kiwon lafiya.