GWAMNA DAUDA LAWAL YA AMINCE ƘARIN ALBASHIN WATA ƊAYA GA MA'AIKATAN ZAMFARA
- Katsina City News
- 30 Dec, 2024
- 73
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da biyan ƙarin albashin wata ɗaya ga ma’aikatan gwamnatin Jihar.
Shugaban ma’aikata na jihar Zamfara ne ya sanar da hakan a wata takardar sanarwa da aka bayar a ranar 28 ga watan Disamba 2024.
Albashin wata na 13 shi ne irinsa na biyu a tarihin jihar Zamfara, inda gwamnatin Lawal ta biya na farko a watan Disambar bara.
Ma’aikatan gwamnatin jihar Zamfara da suka haɗa da waɗanda suka yi ritaya, za su samu alawus na kashi talatin bisa ɗari na albashin su a matsayin garaɓasar ƙarin albashin guda, wanda ya zama albashin 13.
Wannan shiri ya nuna irin yadda aka aminta da ƙwazon ma’aikatan Zamfara ta hanyar ba su tallafin kuɗi a lokacin hutun ƙarshen shekara.
Biyan albashin na watan 13 na ɗaya daga cikin dabaru da dama na ƙarfafa wa ma’aikata gwiwa da bunƙasar tattalin arziki a Jihar Zamfara.
Domin cika alƙawuran da ta ɗauka, gwamnati ta cika sama da Naira biliyan 10 na kuɗaɗen alawus-alawus da ake binta a cikin shekaru 11 da suka gabata, ta kuma amince da mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, tare da tabbatar da biyan albashin ma’aikata kan lokaci.