TARIHIN GANUWAR KATSINA.
- Katsina City News
- 29 Dec, 2024
- 70
Ganuwar Gari, wani babban bangone Wanda ya zagaye Gari, Kuma akayi mashi Kofa ko kyaure guda daya.
Tarihi ya nuna an Fara Gina Ganuwar Katsina a lokacin Mulkin Sarkin Katsina Ali Murabit, wajen Karni na sha biyar ( K15).
Akwai dalilai da dama da suka sa ake gina Ganuwar Gari da suka hada da, Tsaro, Tattalin Arziki, da Kuma addini.
1. TSARO.
Babban dalilin dake sa a Gina Ganuwar Gari shine don a samar da Tsaro a tsakanin Al'ummar Gari.
Ganuwar Katsina ta taimaka kwarai wajen Samar da Tsaro a Katsina musamman lokacin da ake yake yake a da, misali acikin shekarar 1554, Mayakan Songhay sun kawo ma Katsina Hari,a dalilin ginin Ganuwar Katsina ne suka tsaya gefen Gari, Katsina tayi nasara akansu. Hakanan Kuma a lokacin Mulkin Sarkin Katsina Jan Hazo, a shekarar 1671,. Jukunawa sun kawo ma Katsina a dalilin Ganuwar Katsina, Katsinawa sukayi nasara akansu.
A zamanin da lokacin yake yake idan Mahara sun kawo hari kamin su shigo Gari, amfani da Gwauren Tambari, da Kuge da Kuma Yan Shela a sanar da Jamaa cewa ga Mahara nan sun iso. Shi Kuge wani Karfe ne aka buga wa a lokacin wadda kamar umarni na cewa kowa ya fito da Shirin Yaki, Wanda keda alhakin kada Kuge shine Maza Waje. Shi Kuma Gwauren Tambari, shima a na amfani dashi wajen isar da Sakon cewa ga Mahara nan sun shigo Gari. Da sauransu.
2. TATTALIN ARZIKI.
Ana Gina Ganuwar Gari, don ta taimaka wajen bunkasa Tattalin arzikin Gari. Dalilin gini Ganuwar Katsina ne aka samu ingantaccen Tsaro a Katsina Wanda yasa bakin Yan Kasuwa daga sassan Duniya da dama suka rika shigowa Katsina don tafiyar da harkar Kasuwancin su. Misali Buzayen Agades sun zauna a Katsina a lokacin ana Kasuwancin Sahara ( Transharan Trade) inda suka kafa Unguwar Sararin Tsako dake cikin Birnin Katsna. Hakanan ma Zuruar Abulgaisu dake Unguwar Albaba sunzo Katsina adalin Kasuwanci daga Kasar Algeria a inda suka kafa Unguwar Albaba. Hakanan akwai Larabawa Yan Kasuwa da suka yo Hijira daga Kano zuwa Katsina acikin Karni na sha bakwai ( K17) da dai sauransu.
3. TA BANGAREN ADDINI.
Adaliin zaman lafiyar da Ginin Ganuwa ya kawo a Katsina an samu Mayan bakin Malamai da suka rika shigowa Katsina tun daga Karni na sha biyar zuwa na sha bakwai. Misali Sheik Dantakun ya zo Katsina a karshen karni na sha biyar daga Kasashen Magrib,. Hakanan Kuma Kakannin Danmasani sunyo Kaura ne daga Borno zuwa Katsina, amma shi Danmasani an haifeshi a Katsina a Unguwar Masanawa acikin shekarar 1595. Da dai sauransu.
Alh. Musa Gambo.