An rage dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a jihar Katsina.
- Katsina City News
- 13 Sep, 2023
- 934
Daga Muhammad Kabir, Katsina
An ƙara tsawaita dokar hana zirga-zirgar babura da yan ƙurƙurori da aka kafa a wasu yankunan ƙananan hukumomin da ke fama da matsalolin tsaro a jihar Katsina.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa data fito daga ofishin kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida ta fitar a jiya Talata, wacce Tukur Hassan Dan-Ali ya sa ma hannu.
Hakan ya biyo bayan taron majalisar tsaro da ya gudana a ranar Talata 12 ga Satumba a shekarar 2023 a gidan gwamnatin jihar.
Bayan gudanar da taron, a yanzu dokar hana zirga-zirgar Babura da Ƙurƙurori za ta fara aiki ne daga karfe goma na dare zuwa shida na safe a kullum maimakon karfe takwas na yamma zuwa shida na safe da aka saba tun da farko.
Kwamitin Tsaron ya kuma gode wa dukkan mutanen da ke zaune a wadannan kananan Hukumomin bisa hadin kai da goyon bayan da ake ba Gwamnati da Hukumomin tsaro game da wannan doka.
Sanarwar ta cigaba da cewa, Gwamnati na aiwatar da tsare-tsare da kokarin kawo karshen kalubalen tsaro a jihar.
Idan dai za a iya tunawa kananan Hukumomin da wannan doka ta hana zirga-zirgar Babura da Yan ƙurƙurori ya shafa sune, Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Faskari, Sabuwa, Dandume, Danja, Funtua, Ƙafur, Malumfashi, Musawa, Matazu, Bakori, Dutsinma, Kurfi, Kankia da Charanchi.