Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Kashe Sama da Naira Biliyan 10 kan Ayyukan Ruwa a Fadin Kananan Hukumomi Bakwai
- Katsina City News
- 28 Dec, 2024
- 380
Daga Abbas Nasir P R O (STOWASSA)
Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Muhalli a Matsakaitan Birane ta Jihar Katsina (STOWASSA), karkashin jagorancin Babban Daraktanta, Alhaji Ibrahim Lawal Dankaba, ta sanar da kafa kwamitoci masu sa ido don kula da ayyukan samar da ruwa a kananan hukumomi bakwai. Wannan muhimmin shiri, wanda Gwamnatin Jihar Katsina ke daukar nauyi karkashin shirin nan na Samar da ingantaccen ruwan sha da tsaftar muhalli Mai dorewa Wato (NG-SURWASH) a takaice zai lakume sama da naira biliyan 10 don inganta ayyukan samar da ruwa a fadin jihar.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ibrahim Lawal Dankaba, ya jaddada cewa za a fara aikin nan take bayan hutun karshen shekara, duba da cewa gwamnati ta biya kaso 40% na kudin fara aiki ga dukkan ‘yan kwangila. Ya kuma yi kira ga cikakken bin ka’idojin aiki don ganin cewa ayyukan sun yi nasara.
A cewar sanarwar, kwamitocin da za su kula da ayyukan sun hada da shugabannin kananan hukumomi, shugabannin jam’iyyar APC, shugabannin matasa, shugabannin mata, ma’aikatan hukumar STOWASSA, da sauran masu ruwa da tsaki daga al’ummomin da abin ya shafa.
Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., ya himmatu wajen cika alkawarin samar da ruwa mai tsafta ga al’ummar Jihar Katsina.
“Wannan al'amari wani bangare ne na jajircewar gwamna wajen inganta rayuwar al’ummar Jihar Katsina. Mun zabo mutanen da suka cancanta don kula da aikin tare da tabbatar da nasarar kammalarsa,” in ji Dankaba.
Ayyukan na samar da ruwan sha za su hada da gina sababbin bututun ruwa, sabunta na da, gyara tsofaffin bututun ruwa a kananan hukumomi kamar haka: Kankara, Charanchi, Funtuwa, Kafur, Batagarawa, Daura, da Baure.
Ayyukan, wadanda gwamnatin jihar ke gudanarwa karkashin hukumar STOWASSA, suna samun goyon baya daga shirin Samar da ingantaccen ruwa da tsaftar muhalli Mai dorewa Wato (NG-SURWASH) a takaice na Bankin Duniya, wanda yake da nufin samar da ruwa da tsaftar muhalli mai a matsakaitan garuruwa.
Babban Kwamitin Mai Kula da dukkanin Yankunan Shiyyoyin Dan Majalisar Dattawa guda Uku ya kunshi:
1. Alhaji Rabiu Gambo Bakori (Shugaban Kwamitin)
2. Yusuf Abdulkadir Nasarawa (Sakataren Kwamitin)
3. Injiniya Salisu Dahiru Himma
4. Injiniya Muntaka Muhammad Na’iya
5. Arc. Usman Aliyu Hajji
6. Qs. Abdullahi Abdullaziz
7. Alhaji Abdulwahab Sani Stores
8. Hon. Suleman Ahmed Muduru
9. Alhaji Yusuf Shehu Shema
10. Alhaji Abdulrashid Tari Maidabino
11. Alhaji Abubakar Yusuf Bindawa
12. Hajiya Hadiza Manman Danmusa
13. Hajiya Fadila Bala Abdullahi
14.
SAURAN MAMBOBIN GUDA NA KWAMITIN A KANANAN HUMOMIN SUN HADA DA
Kwamitin Kula da aikin na Shiyar Katsina *(KATSINA ZONE):*
*KANANAN HUKUMOMIN BATAGARAWA DA CHARANCHI:*
*BATAGARAWA LG*
1. Hon. Bala Batagarawa (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Hadiza Mamman Danmusa (Sakatariya)
3. Shamsu Sahalu Banbami (Shugaban APC)
4. Babangida Sale (Shugaban Matasa)
5. Haire Musa Ibrahim (Shugabar Mata) da sauran mambobi goma sha hudu (14) a karamar hukumar.
*CHARANCHI LG*
1. Hon. Ibrahim Sani (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Yusuf Abubakar Radda (Shugaban APC)
3. Abdullahi Dangoggo (Shugaban Matasa)
4. Hajiya Zainab Ahmad (Shugabar Mata) da sauran mambobi goma (10) a karamar hukumar
Kwamitin Kula da aikin na Shiyar Daura
*(DAURA ZONE)*
Kananan Hukumomin *DAURA DA BAURE:*
*DAURA LG*
1. Hon. Bala Musa Daura (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Iliyasu Aminu (Sakataren Yanki)
3. Mamman S. Banki (Shugaban APC)
4. Salisu Sallau (Shugaban Matasa)
5. Hajiya Sa’adatu Nahabu (Shugabar Mata) da sauran mambobi goma sha bakwai (17) a karamar hukumar.
*BAURE LG*
1. Hon. Murtala Adamu (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Sani Sule (Shugaban APC)
3. Lirwanu Mamman (Shugaban Matasa)
4. Maryam Shitu (Shugabar Mata) tare da sauran mambobi goma sha daya (11) na karamar hukumar.
Kwamitin Kula da aikin na Shiyar Funtua
(*FUNTUA ZONE*)
Kananan Hukumomi *FUNTUA, KAFUR, da KANKARA:*
*FUNTUA LG*
1. Muntari Sani (Sakataren Yanki)
2. Hon. Lawal Sani (Shugaban Karamar Hukuma)
3. Muhammad Sani (Shugaban APC)
4. Habibu Muhammad (Shugaban Matasa)
5. Talatu Rabi’u (Shugabar Mata) da karin mambobi goma sha shidda (16).
*KAFUR LG*
1. Hon. Garba Kanya (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Sadi Isiyaku (Shugaban APC)
3. Audu Kaura (Shugaban Matasa)
4. Gaje Usman (Shugabar Mata) da wasu karin mambobi goma sha daya (11).
*KANKARA LG*
1. Hon. Anas Isah (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Mansir Ishaq (Shugaban APC)
3. Garba Gambo (Shugaban Matasa)
4. Shugabar Mata na Karamar Hukumar, da kuma sauran mambobi goma sha daya a karamar hukumar.(11).
Babban Daraktan na Hukumar STOWASSA, Alhaji Ibrahim Lawal Dankaba, ya yi kira ga kwamitoci da duk masu ruwa da tsaki su yi aiki tukuru don cimma nasarar wannan babban shirin karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda.