Kwastam Sun Rushe Kwamitin Sintiri Na Kan Iyaka Saboda Zarge-Zargen Cin Zarafi
- Katsina City News
- 25 Dec, 2024
- 263
Katsina Times
Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da rushewar Kwamitin Sintiri na Hadin Gwiwa (JBPT) sakamakon zarge-zargen da suka shafi taimakawa wajen safarar kayayyaki da cin zarafin jama’a.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Abdullahi Maiwada, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya, inda ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da Ofishin Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa (ONSA).
Wannan matakin ya zo ne bayan umarnin da Majalisar Wakilai ta bayar a ranar 11 ga Disamba, inda ta umarci kwamitocinta kan Kwastam da Tsaro su binciki ayyukan Hukumar Kwastam a kan iyakokin ƙasa saboda zarge-zargen hannu a safarar kayayyaki da kuma cin zarafi.
Kwamitocin sun samu umarnin duba rawar da sojojin da ke tare da sintirin kwastam ke takawa, don tabbatar da cewa ayyukansu na tafiya daidai da tsarin doka da kare hakkin ɗan adam.
A cewar Maiwada, rushewar JBPT wani ɓangare ne na ƙoƙarin NCS na ƙarfafa kula da iyakokin ƙasa da kuma sake tsara dabarun aiwatarwa na shekarar 2025. JBPT, wacce aka kafa tare da haɗin gwiwar ƙasashen Najeriya, Jamhuriyar Benin, da Jamhuriyar Nijar, ta kasance wata ƙungiya da aka kafa domin yaƙi da safarar kayayyaki, haramtacci, da sauran manyan laifuka na ƙetaren iyaka.
Maiwada ya jaddada cewa rushe kwamitin haɗingwiwar ba zai yi tasiri ga tsaron kan iyaka ko sauƙaƙe harkokin kasuwanci ba, sai dai ya zama muhimmin mataki na zamani wajen inganta ayyukan Kwastam da kuma ƙarfafa tsaron ƙasa.
“Wannan dabarar na da nufin kawar da cikas da ke cikin harkokin kasuwanci, ƙarfafa tsaron iyakoki, yaƙi da safarar kayayyaki, da kuma sauƙaƙe kasuwancin halal,” in ji shi.
Haka zalika, Babban Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya amince da rage wuraren binciken Kwastam a fadin ƙasa don sauƙaƙe ayyuka da rage cikas ga zirga-zirgar kayayyaki da mutane.
A cewarsa, daga yanzu, ayyukan Kwastam za su dogara da bayanan sirri na gaskiya da kuma dabarun sarrafa haɗari don ƙara inganci da tasiri.
Hukumar ta sake jaddada aniyar ta na ƙarfafa tsaron iyaka da tabbatar da bin ka’idojin kasuwanci na duniya a matsayin wani ɓangare na manufofin gyaranta.