YADDA SHIRIN BANKIN DUNIYA YA INGANTA MAKARANTU A JIHAR KATSINA.
- Katsina City News
- 23 Dec, 2024
- 479
Babu shakka, daya daga cikin ayyukan da bankin duniya da ya samu gagarumar nasara a Najeriya shi ne shirin inganta ilimi da rayuwar yara mata Mai suna AGILE wanda a karkashinsa aka gudanar da ayyuka daban-daban a fannin ilimin yara mata a jihohin Najeriya bakwai. Jihohin sune Katsina, Kaduna, Kano, Kebbi, Borno , Ekiti da Plateau.
Bankin duniya tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi ta tarayya sun zabi wadannan jihohin ne bayan da suka yi nazari sosai kan muhimman bayanai kan shiga makaranta da kuma kammala makaranta a tsakanin yara mata a jihohin. Sun kuma yi la'akari da wanzuwar manufofin ba da damar ilimin yara mata da kuma jajircewar jihohi na inganta ilimin yara mata.
Dokta Mustapha Shehu, Shugaban Shirin AGILE a jihar Katsina
An samu nasarar aiwatar da shirin musamman a jihar Katsina inda aka dabbaka shi a matakai uku. Matakan su ne ‘Inganta wuraren koyo da koyarwa’ da ‘Samar da kyakkyawar yanayin karatu ga ‘ya’ya mata’ da ‘Tabbatar da Ingantattum Tsare-tsare’. Kuma an aiwatar da waɗannan matakan ne tare da gwiwar masu ruwa da tsaki da suka haɗa da iyayennyara da jami'ai masu tafiyar da harkar ilimi a matakin jiha da ƙananan hukumomi da kuma wakilan al'umma.
Matakin farko na shirin na da nufin magance matsalolin dake kawo cikar ga ilimin yara mata. Ya ƙunshi gina sabbin azuzuwa da fadada makarantun firamare da kananan makarantun gaba da sakandare, har ma da manyan makarantun sakandare, game da samar da muhimman kayan aikin da ake bukata domin saukaka koyo da koyarwa a makarantu.
Wannan bangare na aikin AGILE ya kuma kunshi gyara tagogi da kofofi da alluna a azuzuwa da samar da sauran kayayyakin makaranta da kayayyakin koyo da koyarwa domin tabbatar da yanayi mai kyau na karatu na karantarwa. Hakazalika, ya haɗa da samar da tallafi Nan musamman ga ilimin yara mata tare da ƙarfafa iyalai, al'ummomi, da makarantu ta hanyar bada dukkan irin gudunmawar da ta dace.
Bayanan da ofishin aiwatar da shirin AGILE da ke Katsina ya fitar sun nuna cewa ya zuwa yanzu, an gina jimillar makarantun sakandire guda 75 a karkashin wannan aiki. Wannan ya hada da kananan makarantun sakandare 45 da manyan makarantun sakandare 30 a fadin jihar.
Hakazalika, an gina azuzuwa 810 wadanda za su dauki dalibai 32,400. Haka kuma an gina bandakuna 600 da kuma samar da kujeru da tebura guda 10,800 na dalibai, da kujeru da tebura 750 na malamai.
Ta fuskar samar da kayayyakin more rayuwa a makarantun tun daga fara aikin zuwa yau, an gyara bandakuna guda 5,286, yayin da aka gina sabbin bandakuna 718 a makarantun da aka gyara. Haka kuma an gyara azuzuwa 3,209.
Gyaran azuzuwan ya hada da gyara bangaye da kasar azuzuwan da rufi, da tagogi, da kofofi, da kujeru, da tebura, da baranda, da ofisoshin malamai da sauran muhimman ababe a azuzuwan. A cikin makarantun da aka gyara, an gina sabbin azuzuwa 267 don daukar karin dalibai da ake sa ran za'a sanya su a makaranta sakamakon waɗannan gyare-gyaren.
Hakazalika an gina rijiyoyin burtsatse 404 da fanfuna a makarantun da aka gyara, yayin da aka gyara wasu rijiyoyin burtsatse da fanfuna guda 258 a makarantun. Wannan ya taimaka gaya wajen karfafa gwiwar yara mata wajen zuwa makaranta, duba da yadda riga ke inganta tsafta a makarantu.
An gudanar da ayyukan ne da matakan tallafi guda hudu, da suka hada da karamin tallafi wanda ya kama daga Naira miliyan 3.7 zuwa Naira miliyan 6 da aka baiwa makarantun sakandare 578, da babban tallafi na Naira miliyan 23.1 da aka bai wa makarantun sakandire 188 da kuma tallafin Naira miliyon 100 wanda aka baiwa makarantun sakandare 300 a jihar.
Wata takarda daga ofishin shirin AGILE dake Katsina ta bayyana cewa, “na farko shi ne tallafin da ya kai dala 8,000 da dala 12,000 zuwa dala 16,000 da aka baiwa makarantu domin inganta bandakuna da kuma samar da wadataccen ruwan sha a makarantu domin inganta muhallin makarantun." Takardar ta kara da cewa "jimilar kananan makarantun sakandare 578 ne suka sami wannan tallafin wanda aka ajiye a asusun ajiyar banki na Kwamitin Gudanarwar Makarantun (SBMCs) waɗanda suka gudanar da ayyukan a ƙarƙashin ƙa'idojin da aka tsara don tabbatar da rikon amana wajen gudanar da aiyukan.
Kowace al’umma, ta hanyar kwamitin SBMC, ta fito da tsarin inganta makarantu wanda ya yi bayani dalla-dalla kan bukatun kowace makaranta. An gudanar da ayyukan a karkashin wani tsari na bin diddigi domin tabbatar da ingancin aiyukan.
Har ila yau an bayar da wani babban tallafi ga makarantun sakandire 188 inda kowace makaranta ta samu dala 60,000 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 23.1 a lokacin da aka ba kwamitocin SBMC kudaden. Makarantun da suka samu tallafin na da yawan daliban da suka kai 400 kuma an zabo makarantun ne a kananan hukumomin jihar 34.