Mutum 614,937 Sun mutu, an sace Fiye Da Miliyan Biyu Da Dubu Dari Biyu A Cikin Shekara guda A Nijeriya -Rahoton NBS
- Katsina City News
- 19 Dec, 2024
- 174
Fiye da mutane 614,937 'yan Najeriya sun mutu, yayin da aka sace wasu 2,235,954 a fadin kasar nan tsakanin watan Mayu na 2023 zuwa Afrilu 2024, a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS).
Hukumar NBS ta bayyana wannan a jiya cikin rahotonta mai taken “Binciken Laifuka da Fahimtar Tsaro (CESPS)” na 2024, wanda aka gudanar daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024.
Rahoton ya nuna cewa fiye da mutane miliyan 2.2 ne aka sace a fadin kasar, inda aka biya kudin fansa har Naira tiriliyan 2.2, wanda ke nufin kimanin Naira miliyan 2.7 a kowae kudin fansa.
Rahoton ya kuma bayyana cewa adadin kashe-kashe ya fi yawa a yankunan karkara, inda aka samu mutane 335,827 da suka mutu, yayin da aka samu 279,110 a birane.
Masana sun yi imanin cewa, duk da cewa manyan mutane suna fuskantar sace-sace, talakawa a karkara ne suka fi shan wahala.
Nazarin rahoton ya nuna cewa yankin Arewa maso Yamma ya fi kowanne yanki yawan kashe-kashe (206,030), sai Arewa maso Gabas (188,992), yayin da aka samu mafi karanci a Kudu maso Yamma (156,993).
A bangaren sace-sace, rahoton ya nuna cewa Arewa maso Yamma ita ma ce ta fi kowanne yanki yawan sace-sace da adadin mutane 1,220,307, sai Arewa ta Tsakiya (317,387), da Kudu maso Gabas (110,432).
Rahoton ya kara da cewa kaso 82.1 cikin 100 na sace-sace an yi su ne a karkara, inda kaso daya cikin 100 suka mutu, kaso 33 aka sako lafiya, yayin da kaso 31 ke jiran mafita.
Daga cikin Naira tiriliyan 2.2 da aka biya kudin fansa, yankin Arewa maso Yamma ya fi yawan biyan kudin fansa da Naira tiriliyan 1.2; sai yankin Kudu maso Yamma da aka samu mafi karanci da Naira biliyan 146.2.
Rahoton ya kuma nuna cewa kaso 91 cikin 100 na sace-sace ana yin su ne domin samun kudin fansa a matsayin kudi ko wasu fa’idoji.
Daga cikin kashe-kashen, kaso 24 cikin 100 na kashe-kashe a birane, sai kaso 21 cikin 100, sun kasance masu nasaba da rikicin siyasa, yayin da rikice-rikicen kan iyaka suka haifar da kaso 25 cikin 100.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, an samu kararrakin sace motoci 1,567,363 a duk fadin kasar, inda aka fi samun yawansu a jihar Legas (603,756), sai Arewa maso Yamma (462,295) da Arewa maso Gabas (146,144).
Nazarin wuraren zama ya nuna cewa mazauna wuraren da ke da karancin kudin shiga a birane da yankunan karkara sun fi samun matsalar rashin tsaro.
Kwararru sun yi kira ga gwamnati ta magance kalubalen tattalin arziki
Da yake tsokaci kan rahoton, kwararren mai binciken tsaro, Abdullahi Garba, ya ce dole ne gwamnati ta mayar da hankali wajen magance matsalar rashin tsaro tare da daukar matakan magance kalubalen tattalin arziki a kasar.
“Matsalolin tattalin arziki suna yi tasiri sosai ga matasa; idan aka samu kyakkyawar hanyar bunkasa tattalin arzikin matasa, za a rage aikata laifuka,” in ji shi.
Fadar Shugaban Kasa, Sojoji da ‘Yan Sanda sun yi shiru
Fadar Shugaban Kasa ta ki tsokaci kan rahoton a jiya duk da kokarin da aka yi don tuntubar su. Haka nan, kakakin Rundunar Sojojin Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, da sauran jami'an tsaro, ba su bayyana ra'ayinsu ba kan rahoton