DIGRIN JAMI'AR ANNAHADA DA MATSAYINSA
- Katsina City News
- 15 Dec, 2024
- 576
Nazarin jaridun Katsina Times da Taskar Labarai
Gwamnatin Katsina ta fitar da matsaya ga duk wanda za ta bai wa muƙami sai wanda yake da matakin digrin farko, amma inda gizon ke saƙar shi ne, ba a fayyace wane irin digiri ba, kuma daga wace Jami'a?
Bayan wani bincike da jaridar Daily Nigeria ta gudanar a watanni baya, ya sa an dakatar da digrin ƙasashen Togo da Kwatano sakamakon yadda aka gano ana sayen digirin ne kuɗi ƙasa ba labari ba.
Wani digiri da aka daɗe ana ce-ce-ku-ce a kansa shi ne, na Jami'ar ANNAHADA daga jihar Maraɗi a jamhuriyar Nijar.
Ma'aikatar Ilimi ta Nijeriya ta sha fitar da saƙo a kan shi daga baya ta yi shiru sakamakon wata yarjejeniyar ƙasashen ECOWAS, wadda ta ce duk membobin ƙasashen su amince da duk wata Jami'a da ɗayarsu ta yarda da ita.
Matsalar farko, Nijar yanzu ta fice daga ƙungiyar ECOWAS, Ma'aikatar Ilimi ta Nijeriya yanzu za ta dawo da adawarta da digrin Jami'ar ANNAHADA.
Wasu misalai da za mu kawo duk muna da hujjoji a kansu na tabbacin gwamnatin Nijeriya ba ta amince da digrin ANNAHADA domin aiki ba.
A Katsina, wani ma'aikaci a gwamnatin tarayya ya samu ƙarin matsayi, amma a wajen tantance takardunsa aka ga digirin ANNAHADA, dalilin soke muƙamin ke nan.
Shi wannan ma'aikacin, ya yi shekaruyana neman wannan matsayin. Ya yi ta kamun ƙafa wajen manyan mutane, da sun yi waya sai a ce masu matsalar digirin ANNAHADA ne.
A Katsina, wata Jami'a za ta ɗau malamai, wani mai neman aiki ya cancanta gaba da baya, amma yana da digiri na uku daga ANNAHADA. Wannan dalilin ya sa tun a wajen tantancewa aka ce ya faɗi, saboda digirinsa na uku na ANNAHADA ne, kuma da shi yake neman aikin.
A Katsina, wasu yara sun samu aiki a Ma'aikatar Ilimi na koyarwa, alfarma ce wani ya nema masu, amma suna zuwa wajen tantance takardunsu, duk masu digirin ANNAHADA sun dawo gida.
A Katsina, an samar wa wani muƙami, muƙamin ba ya buƙatar takardun zurfin ilimi, sai ya yi kuskuren wajen ba da takardun shaidar kammala karatu, sai ya sanya ya yi karatu a ANNAHADA. A kan wannan aka soke muƙamin a gwamnatin tarayya.
A Katsina yanzu haka wata hukuma ta rubuto wa Ma'aikatar da ke ƙarƙashinta cewa, wasu sun je ANNAHADA sun samo digiri na biyu da na uku, suna neman ƙarin girma da su, Hukumar ta ce sam ba ta yarda da wannan digirin ba.
Bincike mai ƙwari ya tabbatar da wasu jami'o'in har bashin takardar digrin suke bayarwa ka biya a hankali. Kuma dole ka biya.
A tsarin Nijeriya, hukumomi daban-daban ke tantance Jami'a da kwasa-kwasan da za su koyar.
A irin waɗannan jami'o'in za su ba da digiri misali a kan kwamfuta, amma duk Jami'ar kwamfutocinsu uku ne masu aiki, sauran fanko ne don ɗaukar hotuna a nuna.
Yana da kyau gwamnatin Katsina ta riƙa tantance me wane digiri za ta bai wa muƙami? Duk ranar da ta rantsar da wanda yake da digirin Jami'a irin su ANNAHADA, wannan na iya kawo wa jihar wani yamaɗiɗin abin kunya ga jihar da ake kira gidan ilimi a Nijeriya.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar taskar Labarai
@ www.taskarlabarai.com
All in All social media platforms
07043777779. 08057777762
Email.newsthelinks@gmail.com