TATSUNIYA: Labarin Cin Amanar Dan’uwana
- Katsina City News
- 15 Dec, 2024
- 116
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani mutum da yake da ‘ya’ya biyu. Wata rana, mahaifinsu ya tura su je neman furannin kawa, yana mai cewa duk wanda ya kawo fure mafi kyau, shi zai fi samun soyayyarsa, kuma za a yi masa aure.
Da suka tafi, karamin yaron ya tsinki wani kyakkyawan fure. Sai babba ya ga furannin, ya kwace na kanensa, sannan ya kashe shi. Daga nan, ya dawo gida da furannin, kuma mahaifinsu ya ba shi kyautar aure.
Bayan wani lokaci, mahaifinsu ya tambaye shi inda kanensa yake. Sai ya yi masa karya, ya ce ya bar shi a baya, kuma zai dawo ba da jimawa ba. Amma sai aka rasa kanen nasa har tsawon kwanaki biyu. Duk da haka, mahaifinsu ya kawar da kai daga damuwa.
Wata rana, wani boka ya zo wucewa ta dajin da yaron ya mutu. Sai ya tsinci wasu kashi yana hurawa, sai kashin nan ya rera wa boka waka:
Kai bokan nan, kai bokan nan,
Kashina ne kake hurawa.
Baba ya aike mu daji,
Mu samo furannin kawa,
Nawa sun fi na dan’uwana kyau,
Sai ya kwace nawan,
Ya kashe ni.
Da boka ya ji haka, sai ya kai wannan labari ga Sarki. Da Sarki ya hurawa kashin, sai shi ma ya ji wakar:
Kai Sarkin nan, kai Sarkin nan,
Kashina ne kake hurawa.
Baba ya aike mu daji,
Ni da yayana,
Nawa sun fi na dan’uwana kyau,
Sai ya kwace nawan,
Ya kashe ni.
Sarki ya sa aka sanar da jama’ar gari cewa kowa ya taru a kofar fada don gano wanda ya aikata wannan danyen aiki. Amma da aka tambayi kowa, babu wanda ya yarda. Sai Sarki ya ce kowa zai hurawa wutar kashin, domin za a gano mai laifi.
Da mahaifin yaron da aka kashe ya hurawa, sai kashin ya ce:
Kai babana, kai babana,
Kashina ne kake hurawa.
Kai ka aike mu daji,
Mu samo furanni, ni da yayana,
Nawa sun fi nasa kyau,
Sai ya dauke nawan,
Ya kashe ni.
Daga nan, Sarki ya kira babban yaron kuma ya ba shi kashin. Da ya hurawa, sai kashin ya ce:
Kai yayana, kai yayana,
Kashina ne kake hurawa.
Baba ya aike mu daji,
Mu samo furanni,
Nawa sun fi naka kyau,
Sai ka dauke nawan,
Ka kashe ni.
A nan ne Sarki ya bayar da umarnin a kama babban yaron kuma a yi masa hukunci irin na kanensa. Shi ke nan, kurunkus! An magance wanda ya ci amana.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Cin amana kan jawo wulakanci.
- Zafin nema ba shi ke kawo samu ba.
- Idan Allah ya nufi mutum da arziki, babu wanda zai hana.
- Alhaki kare ne, mai shi yake bi.
- Abin da ka shuka, shi za ka girba.
Tushen Labarin: "Litattafin Taskar Tatsuniyoyi" na Dakta Bukar Usman.