ASALIN SARAUTAR YANDAKAN KATSINA.

top-news

 Sarautar Yandaka a Katsina ta samo asalintane tun lokacin Sarakunan Habe, lokacin da Sarkin Katsina Muhammadu Korau (1348-1398) ya kawo tsarin Sarauta a Masarautar Katsina. Tun wancan Lokacin Sarautar Yandaka tana daya daga cikin Manyan Hakimmai masu Fada aji a Masarautar Katsina, Kuma tana daya daga cikin Hakimman Karaga, da suka hada da Durbi, Galadima, Gazobi, Yandaka da sauransu. A lokacin shi Yandaka shine Yandakan Katsina, Kuma Hakimin Yandaka Ruma, wannan ya nuna a lokacin Habe hedikwatar Yandaka a Yandaka Ruma take, sannan gidabshi na mulki Yana Unguwar  Kofar Yandaka dake Yanbata yanzu. Ma'anar Yandaka tana nufin Yandakan Gidan Sarki, watau amintaccen Sarki, Wanda keda ikon shiga Turakar Korau. 

    Sarautar Yandaka Hakimin Dutsinma ta samo asaline tun Lokacin Jihadin Shehu Usman Danfodio na Karni na sha Tara ( K19), lokacin da Malam Ummarun Dallaje da Malam Na Alhaji da Malam Ummarun Dunyawa, suka je Sokoto domin amso Tutar Kaddamar da Jihadi a Kasar Katsina. A lokacin da suka Isa Sokoto sun amso Tutocin a wajen  Shehu Mujaddadi, said umarcesu  da su biya su yi bankwana  wajen dansa Muhammadu Bello. A gidan Muhammadu Bello sun dade basu sadu  da shi ba, sai Malam Na Alhaji da Malam Ummarun Dunyawa sukayi gajen  hakuri  sai suka cewa  Malam Ummarun Dallaje Wanda shine karami a cikinsu ya zauna ya jira Muhammadu Bello, idan ya fito  sai yayi masu bankwana. Daga nan sai suka tafi  basu dade da  tafiya ba sai Allah ya yi wa Muhammadu Bello fitowa, da ya fito   ya tarar  da Malam Ummarun Dallaje Yana jiransa, sai ya ce Allahu Akbar, Malam Ummarun Dallaje idan anyi nasarar Jihadi a Katsina Kai zaka Zama Sarkin Katsina. 

   To daga nan dukkansu Mujahidan ( Flagbearers) suka  shigo Katsina suka ci gaba da Jihadi a Kasar Katsina baki dayanta.  Bayan an Kori Habe sun gudu sun koma Maradi, sai aka raba mukamai ga Shuwagabanin Jihadi, shi Ummarun Dallaje shine ya Zama Sarkin Katsina, sai Ummarun Dunyawa ya Zama Sarkin Sullubawa, shi Kuma Malam Na Alhaji ana Kare Jihadi ya rasu acikin shekarar 1807, to sai aka dauko babban danshi Mai suna Muhammadu Dikko aka bashi Sarautar Magajin Malam, itace ta koma Yandakan Katsina. 

    Ita wannan Sarauta ta Yandakan Katsina da farko  Yandakan Yana zaune a cikin Katsina ne, daga baya ta komaTsauri , sai Kuma daga baya  acikin shekarar 1928, lokacin da aka nada Yandaka Muhammad Sada II a matsayin Yandakan  Katsina, sai Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya taso daga Katsina  yazo Dutsinma, kewayar Kasa, sai ya umarci Yandaka Muhammad Sada II daya dawo da hedikwatar shi a Dutsinma, saboda itace ke tsakiyar Kasar Yandakan Katsina. Anan zaa fahimci  cewa Yandaka Muhammad Sada II shine Yandaka na farko  daya Fara Zama a Garin Dutsinma cikin shekarar 1928. 

  Yandakan Katsina Hakimin Dutsinma yana daya daga cikin Hakimman  guda hudu masu zaben Sarki ( King Makers) a Masarautar Katsina. Kuma a gaba dayan Hakimman Katsina Yandaka shi kadai keda ikon ba Sarkin Katsina hannun su gaisa. 

    TSARIN SUNAYEN WADANDA SUKAYI YANDAKAN KATSINA GIDAN MALAN NA ALHAJI. 

1. Muhammadu Dikko ( Magajin Malam). 
2. Namoda ( shine aka Fara Kira Yandakan Katsina). 
3. Abubakar Dan Muhammadu Dikko
4. Hassan Dan Muhammadu Dikko
5. Muhammadu Sada I Dan Muhammadu Dikko
6. Sule Dan Muhammadu Dikko
7. Zubairu Dan Abubakar
8. Usman Mani dan Hassan
  9. Muhammadu Sada II Dan Usman Mani
10. Shehu dan Usman Mani
11. Muhammadu Lawal dan Dan Sannabi ( jikan Yandaka Usman Mani
12. Abdullahi dan Muhammad Sada II
13. Balan Gogggo Muhammad Dan Muhammad Sada II
14. Alhaji Sada Muhammad Sada, shine Yandakan Katsina na yanzu. 

   Ga jerin Magaddan Yandakan Katsina Hakimin Dutsinma 

1. Yariman Dutsinma
2. Yariman Kuki
3. Gagobi Karofi
4. Magaji Katanga
5. Magaji Rayi
6. Magaji Bagagadi
7. Magaji Dagelawao
8. Magaji Kutawa
9. Magaji Wangarawa
10. Magaji Mahuta
11. Magaji Shema
12. Magaji Nasarawa
13. Magaji Makers
14. Magaji Sanawa
15. Magaji Yan-Shantuna
16. Karare Dabawa. 

Alh. Musa Gambo Kofar soro.